Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Children: Involved in guilt of parents

8 ayoyi · 102 fannoni

Ayoyi game da Involved in guilt of parents

  1. Sauranku da suka ragu za su lalace a ƙasashen abokan gābansu saboda zunubansu; da kuma saboda zunuban kakanninsu.

  2. “ ‘Amma in suka tuba daga zunubansu da zunuban kakanninsu, da cin amanar da suka yi mini, da kuma adawar da suka yi da ni,

  3. waɗanda suka sa na yi adawa da su har da na aika da su ƙasar abokan gābansu, sa’ad da suka ƙasƙantar da zukatansu marasa kaciya, suka kuma biya hukuncin zunubansu,

  4. zan tuna da alkawarina da Yaƙub, da alkawarina da Ishaku, da kuma alkawarina da Ibrahim, zan tuna da ƙasar.

  5. ba za a haɗa ka tare da su a jana’iza ba, gama ka hallaka ƙasarka ka kuma kashe mutanenka. Ba za a ƙara ambaci zuriyarka masu aikata mugunta ba.

  6. A shirya wuri don a yayyanka ’ya’yansa maza saboda zunuban kakanninsu; kada a reno su su gāji ƙasar su cika duniya da biranensu.

  7. “Ga shi, yana nan a rubuce a gabana cewa ba zan ƙyale ba, zan yi cikakken ramuwa; zan yi ramuwa a cinyoyinsu

  8. saboda zunubanku da kuma zunuban kakanninku,” in ji Ubangiji. “Gama sun ƙone turare a kan duwatsu suka kuma ƙazantar da ni a kan tuddai, zan yi musu awo in zuba a cinyoyinsu cikakken ramuwa saboda ayyukansu na dā.”