Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Children: Blessed by Jesus

9 ayoyi · 102 fannoni

Ayoyi game da Blessed by Jesus

  1. Sa’an nan aka kawo yara ƙanana wurin Yesu don yă ɗibiya musu hannuwansa, yă kuma yi musu addu’a. Amma almajirai suka tsawata wa waɗanda suka kawo su.

  2. Yesu ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne.”

  3. Sa’ad da ya ɗibiya musu hannuwansa, sai ya tafi abinsa.

  4. Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yă taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su.

  5. Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.

  6. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”

  7. Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su.

  8. Mutane suna kawo jarirai wurin Yesu don yă taɓa su. Da almajiransa suka ga haka, sai suka kwaɓe su.

  9. Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.