Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Children: Rebellious, punished by the civil power

7 ayoyi · 102 fannoni

Ayoyi game da Rebellious, punished by the civil power

  1. “Duk wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.

  2. “Duk wanda ya saci mutum ya sayar da shi, ko kuwa aka iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi.

  3. “Duk wanda ya la’anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.

  4. In mutum yana da gagararren ɗa mai tawaye, wanda ba ya biyayya ga mahaifinsa da mahaifiyarsa, ba ya kuma jin su sa’ad da suke horonsa,

  5. mahaifinsa da mahaifiyarsa za su kama shi su kawo shi ga dattawa a ƙofar garinsu.

  6. Za su ce wa dattawan, “Wannan ɗanmu gagararre ne, mai tawaye. Ba ya mana biyayya. Mai zari ne, kuma mashayi.”

  7. Sa’an nan dukan mazan garinsa za su jajjefe shi har yă mutu. Dole ku fid da mugu daga cikinku. Dukan Isra’ila kuwa za su ji wannan su kuma ji tsoro.