- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Children
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Da ta buɗe kwandon, sai ta ga yaro yana kuka, ta kuwa ji tausayinsa. Ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin jariran Ibraniyawa ne.”
Sai ’yar’uwarsa ta tambayi ’yar Fir’auna, ta ce, “In tafi in samo ɗaya daga cikin matan Ibraniyawa tă yi miki renon yaron?”
Sai ta amsa ta ce, “I, tafi.” Sai yarinyar ta tafi ta kawo mahaifiyar yaron.
Diyar Fir’auna ta ce mata, “Ɗauki jaririn, ki yi mini renonsa, zan kuwa biya ki.” Saboda haka ta ɗauki yaron, ta yi renonsa.
Sa’ad da ya yi girma, sai ta kawo shi wajen ’yar Fir’auna, ya kuwa zama ɗanta, ta kuma ba shi suna Musa, tana cewa, “Na tsamo shi daga ruwa.”
“Duk wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.
“Duk wanda ya saci mutum ya sayar da shi, ko kuwa aka iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi.
“Duk wanda ya la’anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.
“Kada ku ci zalin gwauruwa, ko maraya.
In kuka yi haka, idan kuma suka yi kuka gare ni, zan ji kukansu.
Zan husata, in kuma kashe ku da takobi; matanku kuma, su ma su zama gwauraye, ’ya’yanku kuwa su zama marayu.
Ubangiji ya ce wa Musa,
“Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Macen da ta yi ciki ta kuma haihu ɗa namiji za tă ƙazantu kwana bakwai, kamar yadda takan ƙazantu a lokacin al’adarta.
A rana ta takwas, za a yi wa yaron kaciya.
Sa’an nan dole macen ta jira kwana talatin don a tsabtacce ta daga zub da jini. Ba za tă taɓa wani abu mai tsarki, ko ta je wuri mai tsarki ba sai kwanakin tsabtaccewarta sun cika.
In ta haifi ’ya ta mace ce, makoni biyu macen za tă ƙazantu kamar yadda takan kasance a lokacin al’adarta. Sa’an nan dole tă jira kwana sittin don a tsabtacce ta daga zub da jininta.
“ ‘Sa’ad da kwanakin tsabtaccewarta don ɗa namiji ko ’ya ta mace suka cika, sai ta kawo ɗan rago bana ɗaya wa firist a bakin ƙofar Tentin Sujada don hadaya ta ƙonawa da tattabara ko kurciya na hadaya don zunubi.
Firist zai miƙa su a gaban Ubangiji don yă yi kafara dominta, sa’an nan tă tsabtacce daga zub da jininta. “ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin macen da ta haifi ɗa namiji ko ’ya ta mace.
In ba za tă iya kawo ɗan rago ba, sai ta kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, ɗaya domin hadaya ta ƙonawa ɗayan kuma domin hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominta, za tă kuwa zama tsabtacciya.’ ”
Sauranku da suka ragu za su lalace a ƙasashen abokan gābansu saboda zunubansu; da kuma saboda zunuban kakanninsu.
“ ‘Amma in suka tuba daga zunubansu da zunuban kakanninsu, da cin amanar da suka yi mini, da kuma adawar da suka yi da ni,
waɗanda suka sa na yi adawa da su har da na aika da su ƙasar abokan gābansu, sa’ad da suka ƙasƙantar da zukatansu marasa kaciya, suka kuma biya hukuncin zunubansu,
zan tuna da alkawarina da Yaƙub, da alkawarina da Ishaku, da kuma alkawarina da Ibrahim, zan tuna da ƙasar.
Duk da haka, sa’ad da suke a ƙasar abokan gābansu, ba zan ƙi su, ko in yi ƙyamarsu, in hallaka su ƙaƙaf, har in karya alkawarina da su ba. Ni ne Ubangiji Allahnsu.
Amma saboda su, zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu, waɗanda na fitar da su daga Masar a idon al’ummai, don in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.’ ”