Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Children

257 ayoyi · 102 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ta sāke yin ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Gama Ubangiji ya ji cewa ba a ƙaunata, ya ba ni wannan shi ma.” Saboda haka ta ba shi suna Simeyon.

  2. Har yanzu ta yi ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Yanzu, a ƙarshe mijina zai manne mini, gama na haifa masa ’ya’ya maza uku.” Saboda haka ta ba shi suna Lawi.

  3. Ta sāke yin ciki, sa’ad da ta haifi ɗa sai ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta ba shi suna Yahuda. Sa’an nan ta daina haihuwa.

  4. Allah ya saurari Liyatu, ta kuwa yi ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na biyar.

  5. Sai Liyatu ta ce, “Allah ya sāka mini saboda na ba da mai hidimata ga mijina.” Saboda haka ta ba shi suna Issakar.

  6. Liyatu ta sāke yin ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na shida.

  7. Sai Liyatu ta ce, “Allah ya ba ni kyauta mai daraja. A wannan lokaci mijina zai darajarta ni, domin na haifa masa ’ya’ya maza shida.” Saboda haka ta ba shi suna Zebulun.

  8. Sai Allah ya tuna da Rahila; ya saurare ta ya kuma buɗe mahaifarta.

  9. Sai ta yi ciki ta kuma haifi ɗa ta ce, “Allah ya ɗauke mini kunyata.”

  10. Ta ba shi suna Yusuf, ta kuma ce, “Bari Ubangiji yă ƙara mini wani ɗa.”

  11. “Bawanka mahaifinmu ya ce mana, ‘Kun san cewa matata ta haifa mini ’ya’ya biyu maza.

  12. Ɗayansu ya tafi daga gare ni, na kuwa ce, “Tabbatacce an yayyage shi kaca-kaca.” Ban kuwa gan shi ba tuntuni.

  13. In kun ɗauki wannan daga wurina shi ma wani abu ya same shi, za ku kawo furfura kaina zuwa kabari cikin baƙin ciki.’

  14. Sai Yaƙub ya kira ’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa.

  15. “Ku tattaru, ku saurara, ’ya’yan Yaƙub maza; ku saurari mahaifinku, Isra’ila.

  16. “Ruben, kai ne ɗan farina, ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina, mafi matsayi, kuma mafi iko.

  17. Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba, gama ka hau gadon mahaifinka ka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi.

  18. “Simeyon da Lawi ’yan’uwa ne, takubansu makamai ne na tā da hankali.

  19. Ba zan shiga shawararsu ba, ba zan shiga taronsu ba, gama sun kashe maza cikin fushinsu cikin ganin dama suka kashe bijimai.

  20. La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai, hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai! Zan warwatsa su cikin Yaƙub in kuma daidaita su cikin Isra’ila.

  21. “Yahuda, ’yan’uwanka za su yabe ka; hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka, ’ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka.

  22. Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda, ka dawo daga farauta, ɗana. Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe, kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?

  23. Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba, ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba, sai ya zo ga wanda yake mai shi. Biyayyar al’umma kuwa tasa ce.

  24. Zai daure jakinsa a kuringa, aholakinsa a rassa mafi kyau; zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabi rigunansa cikin inabi ja wur kamar jini.

  25. Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi, haƙorarsa farare kamar madara.