Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Assyria

204 ayoyi · 59 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. ga abin da maganar Ubangiji ya faɗa a kansa, “Budurwa Diyar Sihiyona ta rena tana kuma maka ba’a. Diyar Urushalima tana kada kai yayinda kake gudu.

  2. Wane ne ka zargi ka kuma yi wa saɓo? A kan wa ka tā da muryarka ka kuma daga idanu cikin fariya? A kan Mai Tsarkin nan na Isra’ila!

  3. Ta wurin jakadunka ka jibge zage-zage a kan Ubangiji. Ka kuma ce, ‘Da kekunan yaƙina masu yawa na hau ƙwanƙolin duwatsu, ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon. Na sassare al’ul mafi tsayi fir mafi kyau. Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa.

  4. Na haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa na kuma sha ruwa a can. Da tafin ƙafafuna na busar da dukan rafuffukan Masar.’

  5. “Ba ka ji ba cewa tun dā can na shirya ya zama haka? A kwanakin dā na kafa shi; yanzu na sa ya faru, cewa ka mai da birane masu mafaka zuwa tsibin ɓuraguzai.

  6. Mutanensu, suka rasa ƙarfi, sun firgita suka kuma sha kunya. Suka zama kamar tsire-tsire a gona, kamar tsire-tsiren ta suka tohu, kamar ciyawar da ya tsiro a kan rufi, wadda zafi ya yi wa ƙuna kafin tă yi girma.

  7. “Amma na san inda kake zama da sa’ad da kakan fita ka kuma koma da yadda ka harzuƙa gāba da ni.

  8. Saboda ka harzuƙa gāba da ni kuma saboda girmankanka ya kai kunnuwana, zan sa ƙugiya a hancinka linzamina a bakinka, zan kuma sa ka koma ta hanyar da ka zo.

  9. “Wannan zai zama alama gare ka, ya Hezekiya, “Wannan shekara za ka ci abin da ya yi girma da kansa, shekara ta biyu kuma abin da ya tsiro daga wancan. Amma a shekara ta uku za ka yi shuki ka kuma girba, za ka dasa gonakin inabi ka kuma ci ’ya’yansu.

  10. Sauran da suka rage na gidan Yahuda kuwa za su yi saiwa a ƙarƙashi su kuma ba da ’ya’ya a bisa.

  11. Gama daga Urushalima raguwa za tă fito, kuma daga Dutsen Sihiyona ƙungiyar waɗanda suka tsira. Himmar Ubangiji Maɗaukaki zai cika wannan.

  12. “Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga wannan birni ba ya harbe kibiya a nan. Ba zai zo gabansa da garkuwa ba ko ya gina mahaurai kewaye a kansa ba.

  13. Ta hanyar da ya zo da ita zai koma; ba zai shiga wannan birni ba,” in ji Ubangiji.

  14. “Zan kāre wannan birni in kuma cece shi, saboda girmana da kuma saboda sunan Dawuda bawana!”

  15. Ta ba da kanta ga duk waɗanda suke masu ilimin Assuriya ta kuma ƙazantar da kanta da dukan gumaka na kowa da take kai da kawowa a cikinsu.

  16. Ba ta bar karuwancin da ta fara a Masar ba, sa’ad da take budurwa maza sun kwana da ita, suka rungumi ƙirjinta suka kuma biya kwaɗayinsu a kanta.

  17. “Saboda haka na bashe ta ga kwartayenta, Assuriyawa, waɗanda ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.

  18. Suka tuɓe ta tsirara, suka kwashe ’ya’yanta maza da mata suka kuma kashe ta da takobi. Ta kuwa zama abin karin magana a cikin mata, aka kuma yi mata hukunci.

  19. “Ƙanuwarta Oholiba kuwa ta ga wannan, duk da haka cikin kai da kawowarta da karuwancinta ta fi ’yar’uwar lalacewa.

  20. Ita ma ta yi ta kai da kawowa cikin Assuriyawa, gwamnoni da manyan sojoji; mayaƙa masu saye da kayan yaƙi, suna bisa dawakai, dukansu samari ne masu bansha’awa.

  21. Na ga cewa ita ma ta ƙazantar da kanta; dukansu biyu sun bi hanya guda.

  22. “Amma karuwancinta ya zarce. Ta ga an zāna mutane a kan bango, siffofin sojojin Kaldiyawa suna cikin jajjayen riguna,

  23. da ɗamara a gindinsu da rawuna a kansu suna kaɗawa falfal; dukansu sun yi kamar jarumawan kekunan yaƙin Babiloniyawa ’yan Kaldiya.

  24. Nan da nan da ta gan su, sai ta yi sha’awarsu ta aika da ’yan aika zuwa wurinsu a Kaldiya.

  25. Sai Babiloniyawan suka zo wurinta, zuwa gadon soyayya, cikin kai da kawowarsu suka ƙazantar da ita. Bayan sun ƙazantar da ita, sai ta ji ƙyamarsu, ta rabu da su.