Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Assyria: Prophecies concerning

91 ayoyi · 59 fannoni

Ayoyi game da Prophecies concerning

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama’arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Efraim daga na Yahuda, zai kawo sarkin Assuriya.”

  2. A wannan rana Ubangiji zai yi feɗuwa yă kira ƙudaje daga rafuffuka masu nisa na Masar da kuma ƙudan zuma daga ƙasar Assuriya.

  3. Za su zo su mamaye kwazazzabai da kogwanni cikin duwatsu, a kan dukan ƙayayyuwa da dukan rammukan ruwa.

  4. A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da rezan da aka yi haya daga ƙetaren Kogi, sarkin Assuriya ke nan, yă aske kanku da gashin ƙafafunku, zai kuma aske gemunku.

  5. A ranar, mutum zai bar karsana ɗaya da awaki biyu da rai.

  6. Kuma saboda yalwa madarar da suke bayarwa, zai kasance da madarar da zai sha. Dukan waɗanda suka rage a ƙasar za su sha madara da zuma.

  7. A wannan rana, a kowane wuri inda akwai kuringa dubu da kuɗinsu ya kai shekel dubu na azurfa, ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne kawai za su kasance a can.

  8. Mutane za su je can da baka da kibiyoyi, gama ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne za su rufe ƙasar.

  9. Game da dukan tuddai da dā ake nome da garemani kuwa, ba za ku ƙara je wurin ba saboda tsoron ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya; za su zama wuraren da ake kai shanu a sake su su yi ta yawo da kansu, tumaki kuma su yi ta gudu.

  10. Kafin yaron yă san yadda zai ce ‘Babana’ ko ‘Mamana,’ sarkin Assuriya zai kwashe arzikin Damaskus da ganimar Samariya.”

  11. Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce,

  12. “Domin wannan jama’a ta ƙi natsattsen ruwan rafin Shilowa suka yi ta farin ciki a kan Rezin ɗan Remaliya,

  13. saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu rigyawar ruwan Kogi, wato, sarkin Assuriya da dukan sojojinsa. Zai cika dukan gaɓoɓinsa, yă kuma malala har zuwa bakin kogi.

  14. Yă yi ta malala har zuwa cikin Yahuda, yă shafe ta, yana ratsa ta ciki har yă kai kafaɗa. Fikafikansa da ya buɗe za su rufe fāɗin ƙasarka, Ya Immanuwel!”

  15. Ku yi kururuwar yaƙi, ku ƙasashe, ku kuma ji tsoro! Ku saurara, dukanku manisantan ƙasashe. Ku shirya don yaƙi, ku kuma ji tsoro!

  16. Ku ƙirƙiro dabarunku, amma ba za su yi nasara ba; ku ƙulla shirye-shiryenku, amma ba za su yi amfani ba, gama Allah yana tare da mu.

  17. “Kaiton Assuriya, sandar fushina, a hannun da kulkin fushina yake!

  18. Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah, na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi, don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima, yă tattake su kamar laka a tituna.

  19. Amma ba abin da ya yi niyya ke nan ba, ba abin da yake da shi a zuciya ba; manufarsa shi ne yă hallaka, yă kuma kawo ƙarshen al’ummai da yawa.

  20. Ya ce, ‘Dukan shugabannin yaƙina ba sarakuna ba ne?’

  21. ‘Kalno bai kasance kamar Karkemish ba? Hamat bai zama kamar Arfad Samariya kuma kamar Damaskus ba?

  22. Yadda hannuna ya ƙwace mulkokin gumaka, mulkokin da siffofinsu suka fi na Urushalima da Samariya,

  23. ba zan yi da Urushalima da siffofinta yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?’ ”

  24. Sa’ad da Ubangiji ya gama dukan aikinsa gāba da Dutsen Sihiyona da Urushalima, zai ce, “Zan hukunta sarkin Assuriya saboda fariya na gangancin zuciyarsa da kuma kallon reni na idanunsa.

  25. Gama ya ce, “ ‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan, da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi. Na kau da iyakokin ƙasashe, na washe dukiyarsu; a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu.