Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Assyria: Insulted and threatened Judah

20 ayoyi · 59 fannoni

Ayoyi game da Insulted and threatened Judah

  1. Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki.

  2. Suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka je wurinsu.

  3. Jagoran dogarawan sarkin Assuriya ya ce musu, “Ku ce wa Hezekiya, “ ‘Ga abin da babban sarkin Assuriya ya ce, da wa kake taƙama?

  4. Ka ce kana da dabara da ƙarfin soji, amma bagu kawai kake yi. Da wa ka dogara har da za ka yi mini tawaye?

  5. Na sani kana dogara da Masar, wadda take kamar karar masara, wadda in ka jingina a kai, za tă karye tă soki hannunka. Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga dukan wanda ya dogara da shi.

  6. Sai ya ci gaba da cewa, in kuma ka ce mini “Muna dogara ga Ubangiji Allahnmu ne,” ba masujadansa da bagadansa ne Hezekiya ya ciccire, yana ce wa Urushalima da Yahuda, “Dole ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima”?

  7. “ ‘Yanzu, ka zo ku shirya da shugabana, sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sami mahayansu!

  8. Yaya za ka yi tsayayya da mafi ƙanƙantan hafsan shugabana, ko da kana dogara da Masar don kekunan yaƙi da mahaya dawakai?

  9. Ban da haka ma, kana gani cewa na zo in hallaka wannan wuri ne ba tare da na ji daga Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya ce da ni in kawo wa wannan ƙasa hari in hallaka ta.’ ”

  10. Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa suka ce wa jagoran dakarun, “Muna roƙonka ka yi wa bayinka magana da harshen Arameyik da yake muna ji. Kada ka yi mana magana da Yahudanci domin kada mutanen da suke bisa katanga su ji!”

  11. Amma shugaban sojojin ya ce, “Ai, ba gare ku da sarkinku kaɗai ne shugabana ya aike ni ba. Amma har ga mutanen da suke zaune a kan katangar birnin, waɗanda za su ci kashinsu, su sha fitsarinsu!”

  12. Sai shugaban sojojin ya yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji muryar babban sarki, sarkin Assuriya!

  13. Ga abin da sarki ya faɗa; kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku. Ba zai iya cetonku daga hannuna ba.

  14. Kada ku yarda Hezekiya yă rinjaye ku cewa ku dogara ga Allah, sa’ad da ya ce da ku, ‘Ba shakka Ubangiji zai cece mu; yana ce da ku birnin nan ba zai faɗa a hannun sarkin Assuriya ba.’

  15. “Kada ku saurari Hezekiya. Ga abin da sarkin Assuriya ya ce, ku shirya zaman lafiya da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci ’ya’yan inabinsa da ’ya’yan ɓaurensa, yă kuma sha ruwa daga randarsa,

  16. har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! “Kada ku saurari Hezekiya, don karya yake muku, sa’ad da ya ce, ‘Ubangiji zai cece mu.’

  17. “Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda, kada ka bar allahn da kake dogara gare shi yă ruɗe ka cewa, ‘Urushalima ba za tă fāɗi a hannun sarkin Assuriya ba.’

  18. Ba shakka ka riga ka ji abin da sarkin Assuriya ya yi da dukan ƙasashe, yana hallaka su gaba ɗaya. Kai kuwa kana ji za a cece ka?

  19. Allolin al’umman da kakannina suka hallaka, sun cece su ne, allolin Gozan, da na Haran, da na Rezef, da kuma na mutane Eden da suke a Tel Assar?

  20. Ina sarkin Hamat, da sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarfayim, ko na Hena da kuma na Iffa?”