Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Assyria: Extent of conquests

12 ayoyi · 59 fannoni

Ayoyi game da Extent of conquests

  1. Akwai allahn wata al’ummar da ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun sarkin Assuriya?

  2. Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarfayim, da na Hena, da na Iffa? Sun cece Samariya daga hannuna?

  3. Wanne a cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa da gare ni? Shugaban sojojin ya kuma ci gaba da cewa, ta yaya Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?”

  4. Ba shakka ka riga ka ji abin da sarkin Assuriya ya yi da dukan ƙasashe, yana hallaka su gaba ɗaya. Kai kuwa kana ji za a cece ka?

  5. Allolin al’umman da kakannina suka hallaka, sun cece su ne, allolin Gozan, da na Haran, da na Rezef, da kuma na mutane Eden da suke a Tel Assar?

  6. Ina sarkin Hamat, da sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarfayim, ko na Hena da kuma na Iffa?”

  7. ‘Kalno bai kasance kamar Karkemish ba? Hamat bai zama kamar Arfad Samariya kuma kamar Damaskus ba?

  8. Yadda hannuna ya ƙwace mulkokin gumaka, mulkokin da siffofinsu suka fi na Urushalima da Samariya,

  9. ba zan yi da Urushalima da siffofinta yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?’ ”

  10. Sa’ad da Ubangiji ya gama dukan aikinsa gāba da Dutsen Sihiyona da Urushalima, zai ce, “Zan hukunta sarkin Assuriya saboda fariya na gangancin zuciyarsa da kuma kallon reni na idanunsa.

  11. Gama ya ce, “ ‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan, da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi. Na kau da iyakokin ƙasashe, na washe dukiyarsu; a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu.

  12. Kamar yadda mutum yakan miƙa hannu cikin sheƙar tsuntsu haka hannuna ya je ya washe dukiyar al’ummai; kamar yadda mutane sukan tattara ƙwai, haka na tattara dukan ƙasashe; ba tsuntsun da ya kakkaɓe fikafiki, ko yă buɗe baki don yă yi kuka.’ ”