Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh Barneya ya ce, “Ku haura ku mallaki ƙasar da na ba ku.” Amma kuka yi tawaye ga umarnin Ubangiji Allahnku. Ba ku amince da shi, ko ku yi masa biyayya ba.

  2. Kun yi ta tawaye wa Ubangiji tun ran da na san ku.

  3. Na kwanta rubda ciki a gaban Ubangiji waɗannan yini arba’in da dare arba’in domin Ubangiji ya ce zai hallaka ku.

  4. Na yi addu’a ga Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kada ka hallaka mutanenka, gādon kanka, da ka fansa ta wurin ikonka mai girma, ka kuma fitar da su daga Masar da hannu mai ƙarfi.

  5. Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Kada ka kula da taurinkan, mugunta da kuma zunubin wannan mutane.

  6. In ba haka ba, ƙasar da ka fitar da mu, za tă ce, ‘Domin Ubangiji bai iya kai su cikin ƙasar da ya yi musu alkawari ba ne, kuma domin ya ƙi su, shi ya sa ya fitar da su ya kashe su a hamada.’

  7. Amma su mutanenka ne, gādonka da ka fitar ta wurin ikonka mai girma, da kuma hannunka mai ƙarfi.”

  8. A lokacin Ubangiji ya ce mini, “Ka sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ka haura wurina a kan dutse. Ka kuma yi akwatin katako.

  9. Ni kuwa zan yi rubutu a kan allunan nan biyu, kalmomin da suke a alluna na farko, waɗanda ka farfashe. Za a ajiye su a cikin akwatin.”

  10. Sai na yi akwatin da itacen ƙirya, na kuma sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, sai na haura dutse da alluna biyun a hannuwana.

  11. Ubangiji kuwa ya sāke yin rubutu a waɗannan alluna abin da ya rubuta a allunan farko, wato, Dokoki Goma da ya furta a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar da mutane suka taru. Sai Ubangiji ya ba ni su.

  12. Sa’an nan na sauko daga dutsen, na kuma ajiye allunan a cikin akwatin da na yi, yadda Ubangiji ya umarce ni, kuma suna can a yanzu.

  13. (Isra’ilawa suka kama hanya daga rijiyoyin Beyerot Bene Ya’akan zuwa Mosera. A can Haruna ya rasu, aka kuma binne shi. Sai Eleyazar ɗansa ya gāje shi a matsayin firist.

  14. Daga can suka tashi zuwa Gudgoda, daga Gudgoda kuma suka tafi Yotbata, ƙasa mai rafuffukan ruwa.

  15. A lokacin Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi don su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yin masa hidima, su kuma sa albarka a cikin sunansa, yadda suke yi har wa yau.

  16. Shi ya sa Lawiyawa ba su da rabo, ko gādo a cikin ’yan’uwansu; Ubangiji ne gādonsu yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)

  17. To, na kasance a kan dutse yini arba’in da dare arba’in kamar yadda dā na yi da farko. Ubangiji kuwa ya saurare ni a wannan lokaci kuma. Ba nufinsa ba ne yă hallaka ku.

  18. Ubangiji ya ce mini, “Ka sauka, ka jagoranci mutanen a hanyarsu, domin su shiga, su kuma mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.”

  19. Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku,

  20. ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba?

  21. Sammai, har da sama sammai, da duniya, da kome da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne.

  22. Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓe ku, ku zuriyarsu, a bisa dukan al’ummai, yadda yake a yau.

  23. Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai.

  24. Gama Ubangiji Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci.

  25. Yakan tsare marayu da gwauraye, yana ƙaunar baƙon da yake zama a cikinku, yana ba su abinci da tufafi.