Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. In kuka lura, kuka kuma kiyaye dukan umarnai da nake ba ku, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma riƙe shi gam,

  2. Ubangiji zai kori dukan waɗannan al’ummai a gabanku, za ku kuma kore al’umman da suka fi ku yawa da ƙarfi.

  3. Duk inda tafin ƙafanku ya taka, zai zama naku; iyakarku zai kama daga hamadan Lebanon da kuma daga Kogin Yuferites zuwa Bahar Rum.

  4. Babu mutumin da zai iya tsayayya da ku. Ubangiji Allahnku, zai sa razana da tsoronku a dukan ƙasar, a duk inda kuka tafi, kamar yadda ya alkawarta muku.

  5. Ga shi, a yau, ina sa a gabanku albarka da kuma la’ana,

  6. albarka in kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, da nake ba ku;

  7. la’ana in ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, kuka kuma juya daga hanyar da na umarce ku, ta wurin bin waɗansu alloli, waɗanda ba ku sani ba.

  8. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da za ku shiga ku ci gādonta, sai ku yi shelar albarkun nan a dutsen Gerizim, ku kuma yi na la’ana a dutsen Ebal.

  9. Waɗannan duwatsu biyu suna a hayin Urdun, yamma da hanya a ƙasar Kan’aniyawa mazaunan Araba, kusa da Gilgal wajajen manyan itatuwan More.

  10. Kuna gab da ƙetare Urdun fa, ku shiga, ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Sa’ad da kuka karɓe ta, kuka kuma zauna a can,

  11. ku tabbata kun yi biyayya da dukan ƙa’idodi, da kuma dokokin da nake sawa a gabanku a yau.

  12. Waɗannan su ne ƙa’idodi da kuma dokokin da za ku lura, ku kuma kiyaye a ƙasar da Ubangiji, Allahn kakanninku, yake ba ku don ku ci gādonta, muddin kuna zama a ƙasar.

  13. Ku hallaka dukan wuraren da al’umman da kuke kora suke yi wa allolinsu sujada, a kan duwatsu masu tsawo, da a kan tuddai, da kuma ƙarƙashin kowane itace gaba ɗaya.

  14. Ku rurrushe bagadansu, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu, ku kuma ƙone ginshiƙan Asheransu da wuta; ku yayyanka gumakan allolinsu, ku kuma shafe sunayensu daga waɗannan wurare.

  15. Ba za ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada a hanyar da suke yi ba.

  16. Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin dukan kabilanku, inda zai sa Sunansa, yă mai wurin mazauninsa. A wannan wuri ne za ku tafi;

  17. a can ne kuma za ku kawo hadayun ƙonawa da sadakoki, zakkarku da kyautai na musamman, da abin da kuka yi alkawari za ku bayar, da hadayunku na yardar rai, da kuma ’ya’yan farin garkunanku na shanu da na tumaki.

  18. A can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku da iyalanku za su ci, su kuma yi farin ciki a kome da kuka sa hannunku a kai, domin Ubangiji Allahnku zai albarkace ku.

  19. Kada ku yi kamar yadda muke yi a nan yau, yadda kowa yake yin abin da ya ga dama.

  20. Gama ba ku kai wurin hutawa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku gādo ba tukuna.

  21. Amma sa’ad da kuka haye Urdun, kuka zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, zai kuwa ba ku hutu daga dukan abokan gābanku da suke kewaye da ku, kuka sami zaman lafiya,

  22. sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato, hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakkarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na alkawarin da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă sa sunansa.

  23. A can kuma za ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, waɗanda ba a ba su rabo ba, ba su kuma da gādo na kansu.

  24. Ku kula fa kada ku miƙa hadayun ƙonawa a wani wurin da kuka ga dama.

  25. Ku miƙa su kawai a wurin da Ubangiji zai zaɓa a cikin ɗaya daga kabilanku, a can za ku yi kowane abin da na umarce ku.