Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Amma kwa iya yanka nama ku ci a garuruwanku, a duk lokacin da ranku yake so, kamar yadda ake yi da gada ko barewa, bisa ga albarkar da Ubangiji Allahnku yake sa muku. Marar tsarki da mai tsarki, duka za ku iya ci.

  2. Amma kada ku ci jini, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.

  3. Kada ku ci zakkar hatsi, da na sabon inabi, da kuma na mai a biranenku, ko kuwa na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki, ko kuwa duk wani abin da kuka yi alkawari za ku bayar, ko hadayunku na yardar rai, ko kyautai na musamman.

  4. A maimakon haka, sai ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, ku kuwa yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a kowane abin da kuka sa hannunku.

  5. Ku yi hankali, kada ku manta da Lawiyawa, muddin kuna zaune a ƙasarku.

  6. Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya fadada iyakarku kamar yadda ya yi muku alkawari, kuka kuma ji marmarin nama, kuka kuma ce, “Muna so mu ci nama,” to, za ku iya cin yadda kuke so.

  7. In wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don yă sa Sunansa yana da nisa sosai daga inda kuke, za ku iya yankan dabbobi daga garkunanku na shanu da na tumakin da Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku, a cikin biranenku kuma za ku iya ci, yadda kuke so.

  8. Ku ci su yadda akan ci barewa ko mariri. Marar tsarki da mai tsarki, za ku iya ci.

  9. Amma ku tabbata ba ku ci jinin ba, domin jini ne rai, ba kuwa za ku ci rai cikin naman ba.

  10. Ba za ku ci jini ba, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.

  11. Kada ku ci shi, don ku zauna lafiya, da ku da ’ya’yanku bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji.

  12. Amma ku ɗauki abubuwa masu tsarki, da kuma duk abin da kuka yi alkawari za ku bayar, ku tafi inda Ubangiji ya zaɓa.

  13. Ku miƙa hadayunku na ƙonawa a bagaden Ubangiji Allahnku, da naman da kuma jinin. Dole a zub da jinin hadayunku a gindin bagaden Ubangiji Allahnku, amma za ku iya cin naman.

  14. Ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan waɗannan umarnan da nake ba ku, da kuma ’ya’yanku, don ku zauna lafiya, da ku da ’ya’yanku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai da kuma yake mai kyau a gaban Ubangiji Allahnku.

  15. Ubangiji Allahnku zai kawar muku da al’umman nan da kuke niyyar shiga cikin ƙasarsu don ku kore su, bayan kuka kore su, kuka kuma zauna a ƙasarsu,

  16. to, sai ku lura, kada ku jarrabtu ku kwaikwaye su bayan da an riga an shafe su daga gabanku, kada ku tambayi kome game da allolinsu, kuna cewa, “Yaya waɗannan al’ummai suke bauta wa allolinsu? Mu ma za mu yi kamar yadda suka yi.”

  17. Ba za ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada a hanyar da suke yi ba, gama a cikin yin sujada wa allolinsu, sun yi dukan abubuwan banƙyaman da Ubangiji yake ƙi. Har ma sukan ƙone ’ya’yansu maza da mata a wuta a matsayin hadayu.

  18. Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku; kada ku ƙara, kada ku rage daga cikin.

  19. In wani annabi ko mai mafarkai, ya bayyana a cikinku, ya kuma yi muku shelar wata alama mai banmamaki ko al’ajabi,

  20. in kuwa alamar, ko al’ajabin da annabin ya yi faɗin ya faru, ya kuma ce, “Bari mu bi waɗansu alloli (allolin da ba ku sani ba) mu kuma yi musu sujada,”

  21. kada ku saurari kalmomin wannan annabi ko mai mafarki. Ubangiji Allahnku yana gwada ku ne don yă sani ko kuna ƙaunarsa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.

  22. Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa.

  23. Dole a kashe wannan annabi ko mai mafarki, domin ya yi wa’azin tawaye ga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, ya fanshe ku daga ƙasar bauta; gama annabin nan ya yi ƙoƙari yă juye daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, ku bi. Dole ku fid da mugu daga cikinku.

  24. In ɗan’uwanka, ko ɗanka, ko ’yarka, ko matar da kake ƙauna, ko abokinka na kusa, a ɓoye ya ruɗe ka, yana cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ko kai, ko kakanninka ba su sani ba,

  25. allolin mutanen kewayenku, ko na kusa, ko na nisa, daga wannan ƙarshen ƙasar zuwa wancan),