- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Maimaitawar Shari’a 13:8kusan 1451 K.H.
kada ka yarda da shi, kada ma ka saurare shi. Kada ka ji tausayinsa. Kada ka haƙura da shi, ko ka tsare shi.
- Maimaitawar Shari’a 13:9kusan 1451 K.H.
Dole ka kashe shi. Dole hannunka yă zama na farko a kisansa, sa’an nan hannuwan sauran dukan mutane.
- Maimaitawar Shari’a 13:10kusan 1451 K.H.
Ku jajjefe shi da duwatsu har sai ya mutu, domin ya yi ƙoƙari yă juye ku daga Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma.
- Maimaitawar Shari’a 13:11kusan 1451 K.H.
Sa’an nan dukan Isra’ila za su ji su kuma tsorata, babu kuma wani a cikinku da zai ƙara yin irin wannan mugun abu.
- Maimaitawar Shari’a 13:12kusan 1451 K.H.
In kuka ji an yi magana a kan wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku zauna a ciki
- Maimaitawar Shari’a 13:13kusan 1451 K.H.
cewa mugaye sun taso a cikinku, suna rikitar da mutane a birni, suna cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ba ku sani ba),
- Maimaitawar Shari’a 13:14kusan 1451 K.H.
to, sai ku bincike labarin sosai a hankali. In kuwa gaskiya ne, an kuma tabbatar wannan abin ƙyama ya faru a cikinku,
- Maimaitawar Shari’a 13:15kusan 1451 K.H.
dole a karkashe dukan waɗanda suke zama a wannan birni da takobi. Ku hallaka su ƙaƙaf, ku karkashe mutanen birnin da kuma dabbobinsa.
- Maimaitawar Shari’a 13:16kusan 1451 K.H.
Ku tattara dukan ganimar birnin a tsakiyar gari, ku ƙone birnin da kuma ganimar ƙurmus a matsayin hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji Allahnku. Birnin zai kasance kufai har abada, kada a sāke gina shi.
- Maimaitawar Shari’a 13:17kusan 1451 K.H.
Ba za a iske wani daga cikin abubuwan nan da aka haramta a hannuwanku ba, saboda Ubangiji yă juya daga fushinsa mai ƙuna, yă nuna jinƙai, yă ji tausayinku, yă kuma ƙara yawanku, kamar yadda ya alkawarta da rantsuwa ga kakanninku,
- Maimaitawar Shari’a 13:18kusan 1451 K.H.
domin kun yi biyayya da Ubangiji Allahnku, kuna kiyaye dukan umarnan da nake ba ku a yau, kuna kuma aikata abin da yake daidai a idanunsa.
- Maimaitawar Shari’a 14:1kusan 1451 K.H.
Ku ’ya’yan Ubangiji Allahnku ne. Kada ku yi wa kanku zāne, ko ku yi wa kanku aski irin da akan bar sanƙo, saboda wanda ya mutu,
- Maimaitawar Shari’a 14:2kusan 1451 K.H.
gama ku jama’a ce mai tsarki ga Ubangiji Allahnku. Daga dukan mutane a fuskar duniya, Ubangiji ya zaɓe ku, ku zama abin mallakarsa.
- Maimaitawar Shari’a 14:3kusan 1451 K.H.
Kada ku ci wani haramtaccen abu.
- Maimaitawar Shari’a 14:4kusan 1451 K.H.
Waɗannan su ne dabbobin da za ku iya ci, saniya, tunkiya, akuya,
- Maimaitawar Shari’a 14:5kusan 1451 K.H.
mariri, barewa, mariya, makwarna, mazo, gada da kuma tunkiyar dutse.
- Maimaitawar Shari’a 14:6kusan 1451 K.H.
Za ku iya cin duk dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take sāke tona abin da suka riga suka haɗiye.
- Maimaitawar Shari’a 14:7kusan 1451 K.H.
Amma, cikin waɗanda suke sāke tona abin da suka riga suka haɗiye ɗin, ko suke da rababben kofato, ba za ku ci raƙumi, zomo ko rema ba. Ko da yake suna sāke tona abin da suka riga suka haɗiye, suna kuma da rababben kofato, su ɗin marar tsarki ne gare ku.
- Maimaitawar Shari’a 14:8kusan 1451 K.H.
Alade ma marar tsarki ne; ko da yake yana da rababben kofato, shi ba ya sāke tona abin da ya riga ya haɗiye. Ba za ku ci namansu ko ku taɓa gawarsu ba.
- Maimaitawar Shari’a 14:9kusan 1451 K.H.
Cikin dukan halittun da suke cikin ruwa, za ku iya cin duk wani da yake da ƙege da ɓamɓaroki.
- Maimaitawar Shari’a 14:10kusan 1451 K.H.
Amma duk wani abin da ba shi da ƙege da ɓamɓaroki, ba za ku ci ba; gama marar tsarki ne gare ku.
- Maimaitawar Shari’a 14:11kusan 1451 K.H.
Za ku iya cin kowane tsuntsu mai tsabta.
- Maimaitawar Shari’a 14:12kusan 1451 K.H.
Amma waɗannan ba za ku ci ba, gaggafa, ungulu, ungulun kwakwa,
- Maimaitawar Shari’a 14:13kusan 1451 K.H.
duki, buga zaɓi, kowace irin shirwa,
- Maimaitawar Shari’a 14:14kusan 1451 K.H.
kowane irin hankaka,