- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446–1406 BC
The Wilderness Years
Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Maimaitawar Shari’a 10:19kusan 1491 K.H.
Sai ku ƙaunaci baƙi, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar.
- Maimaitawar Shari’a 10:20kusan 1491 K.H.
Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku kuma bauta masa. Ku manne masa, ku kuma yi rantsuwarku da sunansa.
- Maimaitawar Shari’a 10:21kusan 1491 K.H.
Shi ne abin yabonku; shi ne Allahnku, wanda ya aikata muku waɗancan manya abubuwa banmamaki masu banrazanar da kuka gani da idanunku.
- Maimaitawar Shari’a 10:22kusan 1491 K.H.
Kakanninku da suka gangara zuwa Masar, su saba’in ne, yanzu kuwa Ubangiji Allahnku ya sa kuka ƙaru, kuka zama kamar taurari a sama.
- Maimaitawar Shari’a 11:1kusan 1491 K.H.
To, sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kullum ku kuma kiyaye abubuwan da yake bukata, ku kiyaye ƙa’idodinsa, dokokinsa da kuma umarnansu.
- Maimaitawar Shari’a 11:2kusan 1491 K.H.
Ku tuna a yau, cewa ’ya’yanku ba su ne suka gani suka kuma ɗanɗana horon Ubangiji Allahnku ba; ba su suka gani girmansa, hannunsa mai ƙarfi, hannunsa mai iko;
- Maimaitawar Shari’a 11:3kusan 1491 K.H.
alamun da ya aikata da abubuwan da ya yi a cikin Masar, ga Fir’auna sarkin Masar da kuma ga dukan ƙasarsa ba;
- Maimaitawar Shari’a 11:4kusan 1491 K.H.
ba su suka gani abin da ya yi wa mayaƙan Masar, da dawakansu da keken yaƙinsu, yadda ya sha kansu da ruwan Jan Teku yayinda suke bin ku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf ba.
- Maimaitawar Shari’a 11:5kusan 1491 K.H.
Ba ’ya’yanku ba ne suka gani abin da ya yi dominku a hamada har sai da kuka kai wannan wuri ba,
- Maimaitawar Shari’a 11:6kusan 1491 K.H.
ba su ba ne suka gani abin da ya yi ga Datan da Abiram, ’ya’yan Eliyab mutumin Ruben, sa’ad da ƙasa ta buɗe bakinta a tsakiyar dukan Isra’ila ta haɗiye su tare da gidajensu, tentunansu da kowane abu mai rai da yake nasu ba.
- Maimaitawar Shari’a 11:7kusan 1491 K.H.
Amma idanunku ne suka ga dukan waɗannan manyan abubuwan da Ubangiji ya yi.
- Maimaitawar Shari’a 11:8kusan 1491 K.H.
Saboda haka sai ku kiyaye dukan umarnan da nake ba ku a yau, don ku sami ƙarfin da za ku shiga, ku kuma karɓi ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaka,
- Maimaitawar Shari’a 11:9kusan 1491 K.H.
domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su da zuriyarsu, ƙasa mai zub da madara da zuma.
- Maimaitawar Shari’a 11:10kusan 1491 K.H.
Ƙasar da kuke shiga, ku karɓa, ba kamar ƙasar Masar ba ce, inda kuka fito, inda kuka shuka iri, ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu.
- Maimaitawar Shari’a 11:11kusan 1491 K.H.
Amma ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaki, ƙasa ce ta duwatsu da kwaruruka wadda ruwan sama ne yake jiƙe ta.
- Maimaitawar Shari’a 11:12kusan 1491 K.H.
Ƙasa ce da Ubangiji Allahnku yake lura da ita; idanun Ubangiji Allahnku yana a kai daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta.
- Maimaitawar Shari’a 11:13kusan 1491 K.H.
Saboda haka in kun yi biyayya ga umarnan da nake ba ku a yau cikin aminci, kuna ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna kuma bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku,
- Maimaitawar Shari’a 11:14kusan 1491 K.H.
sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku.
- Maimaitawar Shari’a 11:15kusan 1491 K.H.
Zan tanadar da ciyawa a filaye don shanunku, za ku ci, ku kuma ƙoshi.
- Maimaitawar Shari’a 11:16kusan 1491 K.H.
Ku yi hankali, kada a ruɗe ku har ku bauta wa alloli, ku kuma yi musu sujada,
- Maimaitawar Shari’a 11:17kusan 1491 K.H.
don kada fushin Ubangiji yă ƙuna a kanku, yă rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku.
- Maimaitawar Shari’a 11:18kusan 1491 K.H.
Saboda haka, sai ku riƙe waɗannan kalmomina gam a zukatanku da ranku; ku ɗaura su kamar alama a hannuwanku, da goshinku.
- Maimaitawar Shari’a 11:19kusan 1491 K.H.
Ku koyar da su ga ’ya’yanku, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
- Maimaitawar Shari’a 11:20kusan 1491 K.H.
Ku rubuta su a kan madogaran ƙofofin gidajenku, da a kan ƙofofinku,
- Maimaitawar Shari’a 11:21kusan 1491 K.H.
saboda kwanakinku da kwanakin ’ya’yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninku, muddin sama tana bisa duniya.