Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 22:30kusan 1452 K.H.

    Jakar ta ce wa Bala’am, “Ni ba jakarka ba ce wadda kake hawa kullum, har yă zuwa yau? Na taɓa yin maka haka?” Bala’am ya ce, “A’a.”

  2. Ƙidaya 22:31kusan 1452 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya buɗe idanun Bala’am, ya kuwa ga mala’ikan Ubangiji tsaye a hanya da takobi a zāre. Sai ya sunkuyar da kansa, ya fāɗi rubda ciki.

  3. Ƙidaya 22:32kusan 1452 K.H.

    Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya tambaye shi, “Don me ka buge jakarka har sau uku? Na fito ne don in hana ka, gama hanyarka ba daidai ba ce a gabana.

  4. Ƙidaya 22:33kusan 1452 K.H.

    Jakar ta gan ni, ta kauce mini har sau uku. Da a ce ba tă kauce ba, lalle da na kashe ka, in kuwa bar ta da rai.”

  5. Ƙidaya 22:34kusan 1452 K.H.

    Bala’am ya ce wa mala’ikan Ubangiji, “Na yi zunubi. Ban san ka tsaya a hanya don ka hana ni ba. Yanzu in ba ka ji daɗin tafiyata, sai in koma.”

  6. Ƙidaya 22:35kusan 1452 K.H.

    Mala’ikan Ubangiji ya ce wa Bala’am, “Ka tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka ne kaɗai za ka faɗa.” Saboda haka Bala’am ya tafi tare da dattawan Balak.

  7. Ƙidaya 22:36kusan 1452 K.H.

    Da Balak ya ji cewa Bala’am yana zuwa, sai ya fito, ya tarye shi a garin Mowabawa da suke a iyakar Arnon, a ƙarshen yankinsa.

  8. Ƙidaya 22:37kusan 1452 K.H.

    Balak ya ce wa Bala’am, “Ban aika maka saƙo cikin gagawa ba? Me ya sa ba ka zo ba? Ko ban isa in sāka maka ba ne?”

  9. Ƙidaya 22:38kusan 1452 K.H.

    Bala’am ya amsa ya ce, “To, ai, ga shi, na zo yanzu. Ina da wani ikon yin wata magana ne? Dole in faɗa abin da Allah ya ce in faɗa ne kawai.”

  10. Ƙidaya 22:39kusan 1452 K.H.

    Sa’an nan Bala’am ya tafi tare da Balak zuwa Kiriyat-Huzot,

  11. Ƙidaya 22:40kusan 1452 K.H.

    a can ya yi hadaya da shanu da tumaki, ya kuwa aika wa Bala’am da dattawan da suke tare da shi.

  12. Ƙidaya 22:41kusan 1452 K.H.

    Kashegari, Balak ya ɗauki Bala’am ya kai shi kan Bamot Ba’al, daga can ya iya ganin sassan sansanin Isra’ilawa.

  13. Ƙidaya 23:1kusan 1452 K.H.

    Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”

  14. Ƙidaya 23:2kusan 1452 K.H.

    Balak ya yi yadda Bala’am ya faɗa, sai su biyu suka miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

  15. Ƙidaya 23:3kusan 1452 K.H.

    Sa’an nan Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in koma wani wurin da yake a kaɗaice. Wataƙila Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Sai ya haura kan wani wurin da yake a kaɗaice a tudun.

  16. Ƙidaya 23:4kusan 1452 K.H.

    Allah kuwa ya sadu da Bala’am. Bala’am ya ce, “Na shirya bagadai bakwai, na kuma miƙa bijimi guda da rago guda, a kan kowane bagade.”

  17. Ƙidaya 23:5kusan 1452 K.H.

    Ubangiji ya ba wa Bala’am saƙo ya ce, “Ka koma wurin Balak, ka faɗa masa wannan saƙo.”

  18. Ƙidaya 23:6kusan 1452 K.H.

    Saboda haka, sai Bala’am ya koma wurin Balak ya same shi tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dukan dattawan Mowab.

  19. Ƙidaya 23:7kusan 1452 K.H.

    Sai Bala’am ya furta abin da Allah ya faɗa masa ya ce, “Balak ya kawo ni daga Aram, sarkin Mowab ya kawo ni daga gabashin duwatsu. Ya ce, ‘Zo, ka la’anta mini Yaƙub; zo, ka tsine Isra’ila.’

  20. Ƙidaya 23:8kusan 1452 K.H.

    Yaya zan iya la’anta waɗanda Allah bai la’anta ba? Yaya zan tsine waɗanda Ubangiji bai tsine ba?

  21. Ƙidaya 23:9kusan 1452 K.H.

    Daga kan duwatsu na gan su, daga bisa kan tuddai na hange su. Na ga mutane da suke zaune su kaɗai ba sa ɗauki kansu ɗaya da al’ummai ba.

  22. Ƙidaya 23:10kusan 1452 K.H.

    Wa zai iya ƙidaya ƙurar Yaƙub ko yă ƙidaya kashi ɗaya bisa huɗu na Isra’ila? Bari in mutu, mutuwar adali ƙarshena kuma yă zama kamar nasu!”

  23. Ƙidaya 23:11kusan 1452 K.H.

    Balak ya ce wa Bala’am, “Me ke nan ka yi mini? Na kawo ka, ka la’anta abokan gābana, sai ga shi albarka kake sa musu!”

  24. Ƙidaya 23:12kusan 1452 K.H.

    Bala’am ya ce, “Ba dole in faɗa abin da Ubangiji ya sa a bakina ba?”

  25. Ƙidaya 23:13kusan 1452 K.H.

    Sa’an nan Balak ya ce masa, “Zo, mu tafi wani wuri inda za ka gan su; a nan kana ganin sashe ne kawai, ba dukansu ba. Daga can kuwa, ka la’anta mini su.”