Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 23:14kusan 1452 K.H.

    Saboda haka ya ɗauke shi zuwa filin Zofim a ƙwanƙolin Fisga, a can ya gina bagadai bakwai, ya kuma miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

  2. Ƙidaya 23:15kusan 1452 K.H.

    Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in je in sadu da Ubangiji a can.”

  3. Ƙidaya 23:16kusan 1452 K.H.

    Ubangiji ya sadu da Bala’am, ya kuma ba shi saƙo ya ce, “Koma wurin Balak ka ba shi wannan saƙo.”

  4. Ƙidaya 23:17kusan 1452 K.H.

    Saboda haka ya tafi ya same Balak tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dattawan Mowab. Balak ya tambaye Bala’am ya ce, “Mene ne Ubangiji ya ce?”

  5. Ƙidaya 23:18kusan 1452 K.H.

    Sai Bala’am ya furta saƙon da aka ba shi ya ce, “Tashi, Balak, ka saurara; ka kasa kunne gare ni, ɗan Ziffor.

  6. Ƙidaya 23:19kusan 1452 K.H.

    Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya, shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa. Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne? Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?

  7. Ƙidaya 23:20kusan 1452 K.H.

    Na karɓi umarni in sa albarka; na kuwa sa albarka, ba zan iya janye ta ba.

  8. Ƙidaya 23:21kusan 1452 K.H.

    “Bai ga mugunta a cikin Yaƙub ba, bai kuma ga wahala a Isra’ila ba. Ubangiji Allahnsu yana tare da su; sowar Sarki yana cikinsu.

  9. Ƙidaya 23:22kusan 1452 K.H.

    Allah ya fitar da su daga Masar; suna da ƙarfi iri na kutunkun ɓauna.

  10. Ƙidaya 23:23kusan 1452 K.H.

    Ba wata maitar da za tă ci Yaƙub, ba sihiri da zai cuci Isra’ila. Yanzu za a ce game da Yaƙub da Isra’ila, ‘Duba abin da Allah ya yi!’

  11. Ƙidaya 23:24kusan 1452 K.H.

    Mutane sun tashi kamar ƙaƙƙarfar zakanya; sun tā da kansu kamar zaki wanda ba ya hutawa sai ya cinye naman abin da ya kama ya kuma sha jinin abin da ya kama.”

  12. Ƙidaya 23:25kusan 1452 K.H.

    Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Kada ka la’anta su, kada kuma ka sa musu albarka!”

  13. Ƙidaya 23:26kusan 1452 K.H.

    Bala’am amsa ya ce, “Ban faɗa maka zan yi kaɗai abin da Ubangiji ya ce ba?”

  14. Ƙidaya 23:27kusan 1452 K.H.

    Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Zo in kai ka wani wuri. Wataƙila zai gamshi Allah, yă bari ka la’anta mini su daga can.”

  15. Ƙidaya 23:28kusan 1452 K.H.

    Balak kuwa ya ɗauki Bala’am zuwa ƙwanƙolin Feyor, wanda yake fuskantar hamada.

  16. Ƙidaya 23:29kusan 1452 K.H.

    Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka kuma shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”

  17. Ƙidaya 23:30kusan 1452 K.H.

    Balak ya yi yadda Bala’am ya ce, ya kuwa miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

  18. Ƙidaya 24:1kusan 1452 K.H.

    To, da Bala’am ya ga cewa Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra’ila albarka, bai koma wajen sihiri kamar dā ba, amma ya juya fuskarsa wajen hamada.

  19. Ƙidaya 24:2kusan 1452 K.H.

    Da Bala’am ya duba sai ya ga Isra’ila sun yi sansani kabila, kabila, Ruhun Allah kuwa ya sauko masa,

  20. Ƙidaya 24:3kusan 1452 K.H.

    sai ya yi annabcinsa ya ce, “Maganar Bala’am ɗan Beyor, saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai,

  21. Ƙidaya 24:4kusan 1452 K.H.

    maganar mutumin da ya saurari maganar Allah, maganar wanda yake ganin wahayi daga Maɗaukaki, mutumin da ya fāɗi rubda ciki, wanda kuma idanunsa suna a buɗe.

  22. Ƙidaya 24:5kusan 1452 K.H.

    “Ina misalin kyan tentunanka, ya Yaƙub, wuraren zamanka, ya Isra’ila!

  23. Ƙidaya 24:6kusan 1452 K.H.

    “Kamar kwaruruka suke a shimfiɗe, kamar lambu kusa da rafi, kamar itatuwan aloyes da Ubangiji ya dasa, kamar itatuwa al’ul kusa da ruwaye.

  24. Ƙidaya 24:7kusan 1452 K.H.

    Ruwa zai kwararo daga bokitinsu; irinsu za su sami ruwa a yalwace. “Sarkinsu zai fi sarkin Agag; mulkinsu zai ɗaukaka.

  25. Ƙidaya 24:8kusan 1452 K.H.

    “Allah ya fitar da su daga Masar; suna da ƙarfin kutunkun ɓauna. Sun cinye abokan gāban, suka kakkarya ƙasusuwansu; da kibiyoyinsu suka sossoke su.