Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446–1406 BC

The Wilderness Years

Forty years of wandering in the desert test Israel's faith and prepare a new generation to enter the promised land.

2,247 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ƙidaya 24:9kusan 1452 K.H.

    Kamar zaki sun laɓe sun kwanta, kamar zakanya, wa zai yi ƙarfin hali yă tashe su? “Bari waɗanda suka albarkace ka, su sami albarka waɗanda kuma suka la’anta ka, su la’antu!”

  2. Ƙidaya 24:10kusan 1452 K.H.

    Fushin Balak ya ƙuna a kan Bala’am. Ya tafa hannunsa, ya ce masa, “Na kira ka don ka la’anta abokan gābana, amma sai ga shi ka sa musu albarka har sau uku.

  3. Ƙidaya 24:11kusan 1452 K.H.

    Yanzu ka bar nan ka tafi gida! Na ce zan sāka maka da lada mai kyau, amma Ubangiji ya hana ka samun ladan.”

  4. Ƙidaya 24:12kusan 1452 K.H.

    Bala’am ya ce wa Balak, “Ban faɗa wa ’yan aikan da ka aiko wurina ba cewa,

  5. Ƙidaya 24:13kusan 1452 K.H.

    ‘Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba, kuma dole in faɗa abin da Ubangiji ya ce ne kawai’?

  6. Ƙidaya 24:14kusan 1452 K.H.

    Yanzu zan koma wajen mutanena, amma bari in gargaɗe ka game da abin da mutanen nan za su yi wa mutanenka cikin kwanaki masu zuwa.”

  7. Ƙidaya 24:15kusan 1452 K.H.

    Sa’an nan ya furta saƙonsa. “Maganar Bala’am ɗan Beyor, saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai,

  8. Ƙidaya 24:16kusan 1452 K.H.

    maganar mutumin da ya saurari maganar Allah, wanda yake da sani daga Mafi Ɗaukaka, wanda yake ganin wahayi daga Maɗaukaki, wanda ya fāɗi rubda ciki, wanda kuma idanunsa suna a buɗe.

  9. Ƙidaya 24:17kusan 1452 K.H.

    “Na gan shi, amma ba yanzu ba; na hange shi, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga Yaƙub; sandan mulki zai fito daga Isra’ila. Zai ragargaje goshin Mowab, kawunan dukan ’ya’yan Set.

  10. Ƙidaya 24:18kusan 1452 K.H.

    Za a ci Edom da yaƙi; za a ci Seyir, abokiyar gābanta, amma Isra’ila zai ƙara ƙarfi.

  11. Ƙidaya 24:19kusan 1452 K.H.

    Mai mulki zai fito daga Yaƙub yă hallaka waɗanda suka ragu a birnin.”

  12. Ƙidaya 24:20kusan 1452 K.H.

    Sai Bala’am ya ga Amalek, ya kuma furta maganarsa. “Amalek yana cikin al’ummai na fari, amma zai zama na ƙarshen da za a hallaka.”

  13. Ƙidaya 24:21kusan 1452 K.H.

    Sai ya ga Keniyawa, ya kuma furta maganarsa. “Wurin zamanku lafiya yake, an kuma sa sheƙarku a cikin duwatsu;

  14. Ƙidaya 24:22kusan 1452 K.H.

    duk da haka, za a hallaka ku Keniyawa sa’ad da Asshur ya kame ku.”

  15. Ƙidaya 24:23kusan 1452 K.H.

    Sai ya furta maganarsa ya ce, “Wayyo, wa zai rayu sa’ad da Allah ya yi haka?

  16. Ƙidaya 24:24kusan 1452 K.H.

    Jiragen ruwa za su zo daga Kittim; za su murƙushe Asshur da Eber, amma su ma za a hallaka su.”

  17. Ƙidaya 24:25kusan 1452 K.H.

    Sa’an nan Bala’am ya tashi ya koma gidan, Balak kuma ya yi tafiyarsa.

  18. Ƙidaya 25:1kusan 1452 K.H.

    Lokacin da Isra’ila suke a sansani a Shittim, sai maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa,

  19. Ƙidaya 25:2kusan 1452 K.H.

    waɗanda suka gayyace su zuwa wajen hadayu na allolinsu. Mutane suka ci suka kuma yi wa waɗannan alloli sujada.

  20. Ƙidaya 25:3kusan 1452 K.H.

    Ta haka Isra’ila suka sa kai a bautar gumaka Ba’al-Feyor. Ubangiji kuwa ya husata da su.

  21. Ƙidaya 25:4kusan 1452 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kama dukan shugabannin mutanen nan, ka kashe su, ka kuma bar su a tsakar rana a gaban Ubangiji, don Ubangiji yă huce daga fushin da nake yi da Isra’ila.”

  22. Ƙidaya 25:5kusan 1452 K.H.

    Saboda haka Musa ya ce wa alƙalan Isra’ila, “Dole kowannenku yă kashe mutanen nan da suka haɗa kai cikin bautar Ba’al-Feyor.”

  23. Ƙidaya 25:6kusan 1452 K.H.

    Sa’an nan wani mutumin Isra’ila ya kawo wata Bamidiyana a iyalinsa a idon Musa da dukan taron jama’ar Isra’ila, yayinda suke kuka a ƙofar Tentin Sujada.

  24. Ƙidaya 25:7kusan 1452 K.H.

    Da Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya ga haka, sai ya bar taron, ya ɗauki māshi

  25. Ƙidaya 25:8kusan 1452 K.H.

    ya bi mutumin Isra’ilan nan cikin tenti, ya soke dukansu biyu, māshin ya ratsa jikin mutumin Isra’ilan har zuwa jikin macen. Sa’an nan aka tsai da annoban nan a kan Isra’ilawa.