- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 4:2kusan 33 M.
Sun damu ƙwarai da gaske domin manzannin suna koya wa mutane suna kuma shela a cikin Yesu cewa akwai tashin matattu.
- Ayyukan Manzanni 4:3kusan 33 M.
Sai suka kama Bitrus da Yohanna, amma da yake yamma ta riga ta yi sai suka sa su cikin kurkuku sai kashegari.
- Ayyukan Manzanni 4:4kusan 33 M.
Amma da yawa da suka ji saƙon suka gaskata, yawan mutanen kuwa ya ƙaru ya kai wajen dubu biyar.
- Ayyukan Manzanni 4:5kusan 33 M.
Kashegari, sai masu mulki, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru a Urushalima.
- Ayyukan Manzanni 4:6kusan 33 M.
Annas babban firist yana nan, haka ma Kayifas Yohanna, Alekzanda da kuma sauran mutanen da suke iyalin babban firist.
- Ayyukan Manzanni 4:7kusan 33 M.
Suka sa aka kawo Bitrus da Yohanna a gabansu suka kuma fara yin musu tambayoyi cewa, “Da wane iko ko da wane suna kuka yi wannan?”
- Ayyukan Manzanni 4:8kusan 33 M.
Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki ya ce musu, “Masu mulki da dattawan mutane!
- Ayyukan Manzanni 4:9kusan 33 M.
In ana tuhumarmu ne yau saboda alherin da aka yi wa gurgun nan da kuma yadda aka warkar da shi,
- Ayyukan Manzanni 4:10kusan 33 M.
to, sai ku san wannan, ku da dukan mutanen Isra’ila cewa da sunan Yesu Kiristi Banazare, wanda kuka gicciye amma wanda Allah ya tasar daga matattu ne, wannan mutum yake tsaye a gabanku lafiyayye.
- Ayyukan Manzanni 4:11kusan 33 M.
Shi ne, “ ‘dutsen da ku magina kuka ƙi, wanda kuwa ya zama dutsen kusurwar gini.’
- Ayyukan Manzanni 4:12kusan 33 M.
Ba a samun ceto ta wurin wani dabam, gama babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka ba wa mutane wanda ta wurinsa dole mu sami ceto.”
- Ayyukan Manzanni 4:13kusan 33 M.
Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu.
- Ayyukan Manzanni 4:14kusan 33 M.
Amma da yake sun ga mutumin da aka warkar yana tsaye a wurin tare da su, sai suka rasa abin faɗi.
- Ayyukan Manzanni 4:15kusan 33 M.
Saboda haka suka umarta a fitar da su daga Majalisar, sa’an nan suka yi shawara da juna.
- Ayyukan Manzanni 4:16kusan 33 M.
Suka ce, “Me za mu yi da waɗannan mutane? Kowa da yake zama a Urushalima ya san sun yi abin banmamaki, kuma ba za mu iya yin mūsu wannan ba.
- Ayyukan Manzanni 4:17kusan 33 M.
Amma don a hana wannan abu daga ƙara bazuwa cikin mutane, dole mu kwaɓe mutanen nan kada su ƙara yi wa kowa magana cikin wannan suna.”
- Ayyukan Manzanni 4:18kusan 33 M.
Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu.
- Ayyukan Manzanni 4:19kusan 33 M.
Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah.
- Ayyukan Manzanni 4:20kusan 33 M.
Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.”
- Ayyukan Manzanni 4:21kusan 33 M.
Bayan ƙarin barazana sai suka bar su su tafi. Ba su iya yanke shawara yadda za a hore su ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.
- Ayyukan Manzanni 4:22kusan 33 M.
Gama mutumin da ya sami warkarwar banmamaki, shekarunsa sun fi arba’in.
- Ayyukan Manzanni 4:23kusan 33 M.
Da aka sake su, Bitrus da Yohanna suka koma wajen mutanensu suka ba da labarin duk abin da manyan firistoci da dattawa suka faɗa musu.
- Ayyukan Manzanni 4:24kusan 33 M.
Sa’ad da suka ji wannan, sai suka ɗaga muryoyinsu gaba ɗaya cikin addu’a ga Allah, suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai ka halicci sama da ƙasa da kuma teku, da kome da yake cikinsu.
- Ayyukan Manzanni 4:25kusan 33 M.
Ka yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin bawanka, kakanmu Dawuda cewa, “ ‘Don me ƙasashe suke fushi, mutane kuma suke ƙulla shawara a banza?
- Ayyukan Manzanni 4:26kusan 33 M.
Sarakunan duniya sun ja dāgā, masu mulki kuma sun taru gaba ɗaya, suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.’