- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 5:15kusan 33 M.
A sakamakon haka, mutane suka kawo marasa lafiya a tituna suka kwantar da su a kan gadaje da tabarmai domin aƙalla inuwar Bitrus za tă bi kan waɗansunsu yayinda yake wucewa.
- Ayyukan Manzanni 5:16kusan 33 M.
Jama’a ma suka tattaru daga garuruwa kewaye da Urushalima suna kawo marasa lafiyarsu da kuma waɗanda mugayen ruhohi suke damun su, dukansu kuwa suka warke.
- Ayyukan Manzanni 5:17kusan 33 M.
Sai babban firist da dukan abokan aikinsa, waɗanda suke na ƙungiyar Sadukiyawa suka cika da kishi.
- Ayyukan Manzanni 5:18kusan 33 M.
Suka kama manzannin suka sa su a kurkukun da ake sa kowa da kowa.
- Ayyukan Manzanni 5:19kusan 33 M.
Amma da dare wani mala’ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun ya fitar da su.
- Ayyukan Manzanni 5:20kusan 33 M.
Ya ce, “Ku je ku tsaya a filin haikali ku sanar wa mutane cikakken saƙon wannan sabon rai.”
- Ayyukan Manzanni 5:21kusan 33 M.
Da gari ya waye, sai suka shiga filin haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane. Sa’ad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya dukan dattawan Isra’ila, suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin.
- Ayyukan Manzanni 5:22kusan 33 M.
Amma da dogarawan suka iso kurkukun, ba su same su a can ba. Saboda haka suka dawo suka ba da labari, suka ce,
- Ayyukan Manzanni 5:23kusan 33 M.
“Mun iske kurkukun a kulle sosai, da masu gadi suna tsaye a bakin ƙofofin; amma da muka buɗe su, sai muka tarar ba kowa a ciki.”
- Ayyukan Manzanni 5:24kusan 33 M.
Da jin wannan labari, sai shugaban masu gadin haikali da manyan firistocin suka ruɗe, suna tunanin abin da wannan al’amari zai zama.
- Ayyukan Manzanni 5:25kusan 33 M.
Sai wani ya zo ya ce, “Ga shi! Mutanen da kuka sa a kurkuku suna tsaye a filin haikali suna koya wa mutane.”
- Ayyukan Manzanni 5:26kusan 33 M.
Da wannan, shugaban ya tafi tare da dogarawansa suka kawo manzannin. Sun kawo su amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada mutane su jajjefe su da duwatsu.
- Ayyukan Manzanni 5:27kusan 33 M.
Da suka kawo manzannin, sai suka sa su suka bayyana a gaban Majalisar don babban firist ya tuhume su.
- Ayyukan Manzanni 5:28kusan 33 M.
Ya ce, “Mun kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa cikin wannan suna, duk da haka kun cika Urushalima da koyarwarku, har ma kuna so ku ɗora mana laifin jinin mutumin nan.”
- Ayyukan Manzanni 5:29kusan 33 M.
Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane!
- Ayyukan Manzanni 5:30kusan 33 M.
Allahn kakanninmu ya tā da Yesu daga matattu, wanda kuka kashe ta wurin ratayewa a bisan itace.
- Ayyukan Manzanni 5:31kusan 33 M.
Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila.
- Ayyukan Manzanni 5:32kusan 33 M.
Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba wa waɗanda suke yin masa biyayya.”
- Ayyukan Manzanni 5:33kusan 33 M.
Da suka ji haka, sai suka yi fushi suka so su kashe su.
- Ayyukan Manzanni 5:34kusan 33 M.
Amma wani Bafarisiyen da ake kira Gamaliyel, wani malamin doka, wanda dukan mutane ke girmamawa, ya miƙe tsaye a Majalisar ya umarta a fitar da mutanen waje na ɗan lokaci.
- Ayyukan Manzanni 5:35kusan 33 M.
Sa’an nan ya yi musu jawabi ya ce, “Mutanen Isra’ila, ku yi kula da kyau da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan.
- Ayyukan Manzanni 5:36kusan 33 M.
Kwanan baya, Teyudas ya ɓullo, yana cewa wai shi wani mutum ne, kuma wajen mutane ɗari huɗu suka bi shi. Aka kuwa kashe shi, dukan masu binsa kuwa suka watse, kome ya wargaje.
- Ayyukan Manzanni 5:37kusan 33 M.
Bayansa, Yahuda mutumin Galili ya ɓullo a kwanakin ƙidaya, ya jagoranci mutane cikin tawaye. Shi ma aka kashe shi, dukan mabiyansa kuma aka watsar da su.
- Ayyukan Manzanni 5:38kusan 33 M.
Saboda haka, a wannan batu na yanzu, ina ba ku shawara. Ku ƙyale mutanen nan! Ku bar su su tafi! Gama in manufarsu ko ayyukansu na mutum ne, ai, zai rushe.
- Ayyukan Manzanni 5:39kusan 33 M.
Amma in daga Allah ne, ba za ku iya hana waɗannan mutane ba, za ku dai sami kanku kuna gāba da Allah ne.”