- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 4:27kusan 33 M.
Tabbatacce Hiridus da Buntus Bilatus suka haɗu tare da Al’ummai da kuma mutanen Isra’ila a wannan birni ce don su ƙulla gāba da bawanka mai tsarki Yesu, wanda ka shafe.
- Ayyukan Manzanni 4:28kusan 33 M.
Sun aikata abin da ikonka da kuma nufinka ya riga ya shirya tuntuni zai faru.
- Ayyukan Manzanni 4:29kusan 33 M.
Yanzu, Ubangiji, ka dubi barazanansu ka kuma sa bayinka su furta maganarka da iyakar ƙarfin hali.
- Ayyukan Manzanni 4:30kusan 33 M.
Ka miƙa hannunka don ka warkar ka kuma yi ayyukan banmamaki da alamu masu banmamaki ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.”
- Ayyukan Manzanni 4:31kusan 33 M.
Bayan suka yi addu’a, sai inda suka taru ya jijjigu. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta shaidar maganar Allah babu tsoro.
- Ayyukan Manzanni 4:32kusan 33 M.
Dukan masu bi kuwa zuciyarsu ɗaya ne, nufinsu kuwa ɗaya. Babu wani da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, amma sun raba kome da suke da shi.
- Ayyukan Manzanni 4:33kusan 33 M.
Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka.
- Ayyukan Manzanni 4:34kusan 33 M.
Babu mabukata a cikinsu. Lokaci-lokaci waɗanda suke da gonaki ko gidaje sukan sayar da su, su kawo kuɗi daga abin da suka sayar,
- Ayyukan Manzanni 4:35kusan 33 M.
su ajiye a sawun manzannin, a kuma raba wa kowa gwargwadon bukatarsa.
- Ayyukan Manzanni 4:36kusan 33 M.
Yusuf, wani Balawe daga Saifurus, wanda manzanni suke kira Barnabas (wanda yake nufin Ɗan Ƙarfafawa)
- Ayyukan Manzanni 4:37kusan 33 M.
ya sayar da wata gonar da ya mallaki ya kuma kawo kuɗin ya ajiye a sawun manzanni.
- Ayyukan Manzanni 5:1kusan 33 M.
To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa.
- Ayyukan Manzanni 5:2kusan 33 M.
Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni.
- Ayyukan Manzanni 5:3kusan 33 M.
Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin?
- Ayyukan Manzanni 5:4kusan 33 M.
Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”
- Ayyukan Manzanni 5:5kusan 33 M.
Da Ananiyas ya ji wannan, sai ya fāɗi ya mutu. Sai babban tsoro kuwa ya kama duk waɗanda suka ji abin da ya faru.
- Ayyukan Manzanni 5:6kusan 33 M.
Sai samari suka zo gaba, suka naɗe gawarsa, suka fitar da shi suka je suka binne.
- Ayyukan Manzanni 5:7kusan 33 M.
Bayan kusan awa uku, sai matarsa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba.
- Ayyukan Manzanni 5:8kusan 33 M.
Bitrus ya tambaye ta ya ce, “Gaya mini, kuɗin da yake da Ananiyas kuka sayar da filin ke nan?” Ta ce, “I, haka ne muka sayar.”
- Ayyukan Manzanni 5:9kusan 33 M.
Bitrus ya ce mata, “Ta yaya kuka yarda ku gwada Ruhun Ubangiji? Duba! Sawun mutanen da suka binne mijinki suna bakin ƙofa, za su kuwa ɗauke ki zuwa waje ke ma.”
- Ayyukan Manzanni 5:10kusan 33 M.
Nan take ta fāɗi a ƙafafunsa ta mutu. Sai samarin suka shigo ciki, suka kuwa same ta matacciya, suka ɗauke ta suka kai ta waje suka binne ta kusa da mijinta.
- Ayyukan Manzanni 5:11kusan 33 M.
Babban tsoro ya kama dukan ikkilisiya da kuma duk wanda ya ji game da abubuwan nan.
- Ayyukan Manzanni 5:12kusan 33 M.
Manzannin suka yi ayyukan da alamu masu banmamaki masu yawa a cikin mutanen. Dukan masu bi kuwa sukan taru a Shirayin Solomon.
- Ayyukan Manzanni 5:13kusan 33 M.
Ba wanda ya yi karambanin shiga cikinsu, duk da haka mutane suna girmama su ƙwarai.
- Ayyukan Manzanni 5:14kusan 33 M.
Duk da haka, maza da matan da suke gaskata ga Ubangiji sai ƙaruwa suke, suka kuma ƙaru a yawa.