Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 40:16kusan 1491 K.H.

    Musa ya aikata dukan kome yadda Ubangiji ya umarce shi.

  2. Fitowa 40:17kusan 1491 K.H.

    Da haka aka kafa tabanakul, a rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu.

  3. Fitowa 40:18kusan 1491 K.H.

    Sa’ad da Musa ya kafa tabanakul, ya sa rammuka a wurinsu, ya sa katakan, ya kuma sa sandunan, ya kakkafa dogayen sandunan.

  4. Fitowa 40:19kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ya shimfiɗa tentin a bisa tabanakul, ya kuma sa murfi a bisa tentin, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  5. Fitowa 40:20kusan 1491 K.H.

    Ya ɗauki dokokin Alkawari ya sa a cikin akwatin, ya kuma zura sandunan a zoban akwatin, sa’an nan ya sa murfin kafara a bisansa.

  6. Fitowa 40:21kusan 1491 K.H.

    Sai ya kawo akwatin a cikin tabanakul, ya kuma rataye labulen rufewa ya tsare akwatin Alkawarin, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  7. Fitowa 40:22kusan 1491 K.H.

    Musa ya sa teburin a Tentin Sujada, a gefen arewa na tabanakul waje da labulen.

  8. Fitowa 40:23kusan 1491 K.H.

    Ya shirya burodin a kai a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  9. Fitowa 40:24kusan 1491 K.H.

    Ya sa wurin ajiye fitilan a Tentin Sujada ɗaura da teburin a gefen kudu na tabanakul

  10. Fitowa 40:25kusan 1491 K.H.

    ya kuma shirya fitilun a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  11. Fitowa 40:26kusan 1491 K.H.

    Musa ya sa bagaden zinariya a cikin Tentin Sujada a gaban labulen

  12. Fitowa 40:27kusan 1491 K.H.

    ya ƙone turare mai ƙanshi a kai, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  13. Fitowa 40:28kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ya sa labule a ƙofar shiga na tabanakul.

  14. Fitowa 40:29kusan 1491 K.H.

    Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  15. Fitowa 40:30kusan 1491 K.H.

    Ya sa daro tsakanin Tentin Sujada da bagade, ya kuma zuba ruwa a cikinsa don wanki,

  16. Fitowa 40:31kusan 1491 K.H.

    a cikin kuwa Musa da Haruna da ’ya’yansa maza sukan wanke hannunsa da ƙafafunsu.

  17. Fitowa 40:32kusan 1491 K.H.

    Sukan yi wanka a duk sa’ad da suka shiga Tentin Sujada, ko in suka kusaci bagade, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  18. Fitowa 40:33kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Musa ya yi fili kewaye da tabanakul da kuma bagaden, ya rataye labule a ƙofar shiga filin. Da haka Musa ya gama aikin.

  19. Fitowa 40:34kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan girgije ya rufe Tentin Sujada sai ɗaukakar Ubangiji ta cika tabanakul.

  20. Fitowa 40:35kusan 1491 K.H.

    Musa bai iya shiga Tentin Sujada ba domin girgije ya riga ya sauka a kansa, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika tabanakul.

  21. Fitowa 40:36kusan 1491 K.H.

    Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul.

  22. Fitowa 40:37kusan 1491 K.H.

    Idan girgijen bai tashi ba, ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi.

  23. Fitowa 40:38kusan 1491 K.H.

    Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan tabanakul da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani.

  24. Firistoci 1:1kusan 1490 K.H.

    Ubangiji ya kira Musa ya yi masa magana daga cikin Tentin Sujada ya ce,

  25. Firistoci 1:2kusan 1490 K.H.

    “Yi magana da Isra’ilawa ka ce musu, ‘Duk sa’ad da waninku ya kawo hadaya ga Ubangiji, ku kawo hadayarku ta dabba daga garkenku ta shanu ko kuwa daga tumakinku.