- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Fitowa 39:34kusan 1491 K.H.
murfi na fatun rago wanda aka rina ja, da murfi na fatun shanun teku; da kuma laɓulen
- Fitowa 39:35kusan 1491 K.H.
akwatin Alkawari da sandunansa da murfin kafara;
- Fitowa 39:36kusan 1491 K.H.
tebur da dukan kayayyakinsa, da burodin Kasancewa;
- Fitowa 39:37kusan 1491 K.H.
wurin ajiye fitilu na zinariya zalla, da jerin fitilunsa da dukan kayayyakinsa, da man fitila,
- Fitowa 39:38kusan 1491 K.H.
bagade na zinariya, da man shafewa, da turare mai ƙanshi, da labulen ƙofar shiga tenti,
- Fitowa 39:39kusan 1491 K.H.
bagade na tagulla na raga, da sandunansa da kayan aikinsa; da daro da wurin ajiyarsa,
- Fitowa 39:40kusan 1491 K.H.
labulen filin, sandunansa da rammukansa, labulen ƙofar shiga filin; igiyoyi da ƙarafan kafa filin; dukan kayan aikin tabanakul da Tentin Sujada;
- Fitowa 39:41kusan 1491 K.H.
da kuma saƙaƙƙun rigunan da ake sawa don hidima a wuri mai tsarki, duk da tsarkakan riguna na Haruna firist da rigunan ’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci.
- Fitowa 39:42kusan 1491 K.H.
Isra’ilawa suka yi dukan aikin nan yadda Ubangiji ya umarci Musa.
- Fitowa 39:43kusan 1491 K.H.
Musa ya duba aikin, sai ya ga cewa sun yi shi daidai yadda Ubangiji ya umarta. Sai Musa ya sa musu albarka.
- Fitowa 40:1kusan 1491 K.H.
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,
- Fitowa 40:2kusan 1491 K.H.
“Ka kafa tabanakul, da Tentin Sujada, a kan rana ta fari ga watan fari.
- Fitowa 40:3kusan 1491 K.H.
Ka sa akwatin Alkawari a cikinsa, sa’an nan ka rufe shi da labule.
- Fitowa 40:4kusan 1491 K.H.
Ka shigar da teburin ka shirya kayayyakin a kansa. Sa’an nan ka shigar da wurin ajiye fitilan ka kuma sa fitilunsa.
- Fitowa 40:5kusan 1491 K.H.
Ka sa bagaden zinariya na ƙona turare a gaban akwatin Alkawari, ka kuma sa labule a ƙofar shiga tabanakul.
- Fitowa 40:6kusan 1491 K.H.
“Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar tabanakul, da Tentin Sujada;
- Fitowa 40:7kusan 1491 K.H.
ka ajiye daron tsakanin Tentin Sujada da bagaden, ka kuma zuba ruwa a cikinsa.
- Fitowa 40:8kusan 1491 K.H.
Ka yi fili kewaye da shi, ka kuma sa labule a ƙofar shiga filin.
- Fitowa 40:9kusan 1491 K.H.
“Ka ɗauki man shafewa ka shafe tabanakul da duka abin da yake cikinsa; ka keɓe shi da dukan kayayyakinsa, zai zama tsarkake.
- Fitowa 40:10kusan 1491 K.H.
Sa’an nan ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da kayansa; ka keɓe bagaden, zai zama mai tsarki.
- Fitowa 40:11kusan 1491 K.H.
Ka shafe daron da wurin ajiyarsa, ka kuma keɓe su.
- Fitowa 40:12kusan 1491 K.H.
“Ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka wanke su da ruwa.
- Fitowa 40:13kusan 1491 K.H.
Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist.
- Fitowa 40:14kusan 1491 K.H.
Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi.
- Fitowa 40:15kusan 1491 K.H.
Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.”