Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 39:9kusan 1491 K.H.

    Ƙyallen maƙalawa a ƙirjin murabba’i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya-ɗaya ne.

  2. Fitowa 39:10kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na farko akwai yakutu, da tofaz, da zumurrudu;

  3. Fitowa 39:11kusan 1491 K.H.

    a jeri na biyu akwai turkuwoyis, da saffaya, da daimon;

  4. Fitowa 39:12kusan 1491 K.H.

    a jeri na uku akwai yakinta, da idon mage, da ametis;

  5. Fitowa 39:13kusan 1491 K.H.

    a jeri na huɗu akwai beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya.

  6. Fitowa 39:14kusan 1491 K.H.

    Aka zāna duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowane sunan ’ya’yan Isra’ila goma sha biyu, kamar yadda akan yi hatimi.

  7. Fitowa 39:15kusan 1491 K.H.

    Sai suka yi tuƙaƙƙun sarƙoƙi na zinariya zalla a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

  8. Fitowa 39:16kusan 1491 K.H.

    Suka yi tsaiko biyu na zinariya da zoban zinariya biyu, suka kuma ɗaura zoban a kusurwoyi biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

  9. Fitowa 39:17kusan 1491 K.H.

    Suka ɗaura sarƙoƙi biyu na zinariya da kusurwoyi na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

  10. Fitowa 39:18kusan 1491 K.H.

    Suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa’an nan suka rataya su a kafaɗun efod daga gaba.

  11. Fitowa 39:19kusan 1491 K.H.

    Suka yi zobai biyu na zinariya suka haɗa, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da efod.

  12. Fitowa 39:20kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan suka yi waɗansu ƙarin zobai biyu na zinariya, suka maƙale su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na efod kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar efod.

  13. Fitowa 39:21kusan 1491 K.H.

    Suka ɗaura zoban ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a zoban efod da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar efod don kada yă kunce daga efod, sun yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  14. Fitowa 39:22kusan 1491 K.H.

    Suka kuma saƙa taguwa ta efod da shuɗi duka, aikin gwani mai saƙa,

  15. Fitowa 39:23kusan 1491 K.H.

    an yi wa taguwar wuyan wundi a tsakiya kamar sulke, aka daje wuyan don kada yă kece.

  16. Fitowa 39:24kusan 1491 K.H.

    Suka yi fasalin ’ya’yan rumman da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da lallausan lilin kewaye da gefe-gefen taguwar.

  17. Fitowa 39:25kusan 1491 K.H.

    Suka yi ƙararrawa da zinariya zalla, suka sa su a tsakanin fasalin ’ya’yan rumman kewaye da gefe-gefen taguwa.

  18. Fitowa 39:26kusan 1491 K.H.

    Aka jera ƙararrawan da ’ya’yan rumman bi da bi. Haka aka jera su kewaye da gefe-gefen taguwar aiki, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  19. Fitowa 39:27kusan 1491 K.H.

    Suka saƙa doguwar riga da lallausan lilin don Haruna da ’ya’yansa, aikin gwani mai saƙa,

  20. Fitowa 39:28kusan 1491 K.H.

    suka yi rawanin da lallausan lilin, da hulan lilin da rigunan ciki na lallausan lilin.

  21. Fitowa 39:29kusan 1491 K.H.

    Suka yi abin ɗamara da lallausan lilin da shuɗi, shunayya da jan zare, aikin gwanin mai ɗinki, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  22. Fitowa 39:30kusan 1491 K.H.

    Suka yi allo tsattsarka da zinariya tsantsa, suka zāna rubutu irin na hatimi a kansa haka, Mai tsarki ga Ubangiji.

  23. Fitowa 39:31kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan suka ɗaura shi da shuɗiyar igiya a gaban rawanin, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  24. Fitowa 39:32kusan 1491 K.H.

    Ta haka aka gama dukan aikin tabanakul da Tentin Sujada. Isra’ilawa suka yi kome yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  25. Fitowa 39:33kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan suka kawo wa Musa tabanakul, tentin da dukan kayayyakinsa, ƙugiyoyinsa, katakansa, da sandunansa, da dogayen sandunansa da rammukansa;