- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Firistoci 2:11kusan 1490 K.H.
“ ‘Kowace hadaya ta garin da kuka kawo ga Ubangiji, dole a yi shi ba tare da yisti ba, gama ba za ku ƙone wani yisti, ko zuma a cikin hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta ba.
- Firistoci 2:12kusan 1490 K.H.
Za ku iya kawo su ga Ubangiji kamar hadaya ta ’ya’yan fari, amma ba za a miƙa su a bagade kamar turare mai ƙanshi ba.
- Firistoci 2:13kusan 1490 K.H.
A sa gishiri a dukan hadayunku na hatsi. Kada a rasa sa gishirin alkawari na Allahnku a hadayunku na hatsi, a sa gishiri a dukan hadayunku.
- Firistoci 2:14kusan 1490 K.H.
“ ‘In kuka kawo hadaya ta gari na ’ya’yan fari ga Ubangiji, sai ku miƙa ɓarzajjen kawunan sabon hatsin da aka gasa a wuta.
- Firistoci 2:15kusan 1490 K.H.
A sa mai da turare a kansa, hadaya ce ta hatsi.
- Firistoci 2:16kusan 1490 K.H.
Firist zai ƙone sashe na ɓarzajjen hatsin da kuma mai, tare da turare don tunawa, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
- Firistoci 3:1kusan 1490 K.H.
“ ‘In hadayar wani mutum, hadaya ta salama ce, ya kuma miƙa ’yar dabba daga garke, ko namiji ko ta mace ce, sai yă miƙa dabbar da ba ta da lahani a gaban Ubangiji.
- Firistoci 3:2kusan 1490 K.H.
Yă kuma ɗibiya hannunsa bisa kan hadayarsa, yă yanka ta a mashigin Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna waɗanda suke firistoci za su yayyafa jinin a kan bagade a kowane gefe.
- Firistoci 3:3kusan 1490 K.H.
Daga hadaya ta zumuncin da zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta; wato, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki ko kuwa da sun shafe su,
- Firistoci 3:4kusan 1490 K.H.
da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
- Firistoci 3:5kusan 1490 K.H.
’Ya’yan Haruna za su ƙone shi a kan bagade a bisa hadaya ta ƙonawa wadda take a kan itacen da yake cin wuta, kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
- Firistoci 3:6kusan 1490 K.H.
“ ‘In ya miƙa dabba ce daga garke a matsayin hadaya ta salama ga Ubangiji, zai miƙa namiji ko ta mace marar lahani.
- Firistoci 3:7kusan 1490 K.H.
In ya miƙa ɗan rago ne, zai kawo shi a gaban Ubangiji.
- Firistoci 3:8kusan 1490 K.H.
Zai ɗibiya hannu a kan hadayarsa, yă yanka shi a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jinin dabbar a kowane gefe na bagade.
- Firistoci 3:9kusan 1490 K.H.
Daga hadaya ta zumuncin zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, kitsen, ƙibabbiya wutsiyar gaba ɗaya da ya yanka gab da ƙashin gadon baya, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, ko kuwa da suka shafe su,
- Firistoci 3:10kusan 1490 K.H.
da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
- Firistoci 3:11kusan 1490 K.H.
Firist zai ƙone su a kan bagade kamar hadayar abinci, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
- Firistoci 3:12kusan 1490 K.H.
“ ‘In yana miƙa akuya ce, zai kawo ta a gaban Ubangiji.
- Firistoci 3:13kusan 1490 K.H.
Zai ɗibiya hannunsa a kanta yă kuma yanka ta a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jininta a kowane gefe na bagade.
- Firistoci 3:14kusan 1490 K.H.
Daga abin da zai miƙa sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, dukan kitsen da ya rufe kayan cikin, ko kuwa da suka shafe su,
- Firistoci 3:15kusan 1490 K.H.
da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
- Firistoci 3:16kusan 1490 K.H.
Firist zai ƙone su a kan bagade kamar abinci, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi. Dukan kitsen na Ubangiji ne.
- Firistoci 3:17kusan 1490 K.H.
“ ‘Wannan dawwammamiyar farilla ce ga tsararraki masu zuwa, a inda za ku zauna. Ba za ku ci wani kitse ko wani jini ba.’ ”
- Firistoci 4:1kusan 1490 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa,
- Firistoci 4:2kusan 1490 K.H.
“Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da wani ya yi zunubi ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji,