Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ibraniyawa 13:15kusan 64 M.

    Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.

  2. Ibraniyawa 13:16kusan 64 M.

    Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.

  3. Ibraniyawa 13:17kusan 64 M.

    Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.

  4. Ibraniyawa 13:18kusan 64 M.

    Ku yi mana addu’a. Mun tabbata cewa muna da lamiri mai kyau, kuma muna da marmari mu yi rayuwa ta bangirma a ta kowace hanya.

  5. Ibraniyawa 13:19kusan 64 M.

    Ni musamman, ina roƙonku ku yi addu’a, don a komo da ni a gare ku ba da daɗewa ba.

  6. Ibraniyawa 13:20kusan 64 M.

    Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya tā da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma,

  7. Ibraniyawa 13:21kusan 64 M.

    yă kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma yă aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin.

  8. Ibraniyawa 13:22kusan 64 M.

    ’Yan’uwa, ina roƙonku ku yi haƙuri da wannan gargaɗi, don ba wata doguwar wasiƙa ce na rubuta muku ba.

  9. Ibraniyawa 13:23kusan 64 M.

    Ina so ku san cewa an saki ɗan’uwanmu Timoti. In ya iso da wuri, zan zo tare da shi in gan ku.

  10. Ibraniyawa 13:24kusan 64 M.

    Ku gai da dukan shugabanninku da kuma dukan mutanen Allah. Waɗanda suke Italiya suna gaishe ku.

  11. Ibraniyawa 13:25kusan 64 M.

    Alheri yă kasance da ku duka.

  12. Yaƙub 1:1kusan 60 M.

    Yaƙub, bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Kiristi, Zuwa ga kabilan nan goma sha biyu, da suke warwartse a cikin al’ummai. Gaisuwa mai yawa.

  13. Yaƙub 1:2kusan 60 M.

    Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku,

  14. Yaƙub 1:3kusan 60 M.

    domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa.

  15. Yaƙub 1:4kusan 60 M.

    Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.

  16. Yaƙub 1:5kusan 60 M.

    In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.

  17. Yaƙub 1:6kusan 60 M.

    Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa.

  18. Yaƙub 1:7kusan 60 M.

    Kada irin wannan mutum yă yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji;

  19. Yaƙub 1:8kusan 60 M.

    shi mai zuciya biyu ne, marar tsai da zuciyarsa wuri ɗaya a cikin duk abin da yake yi.

  20. Yaƙub 1:9kusan 60 M.

    Bari ɗan’uwan da yake cikin halin ƙasƙanci yă yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka.

  21. Yaƙub 1:10kusan 60 M.

    Amma wanda yake mai arziki, ya kamata yă yi taƙama a matsayinsa na ƙasƙanci, gama ba zai daɗe ba kamar furen jeji.

  22. Yaƙub 1:11kusan 60 M.

    Gama in rana ta fito ta yi zafi mai tsanani sai ta sa tsiro yă yanƙwane tsiro; furensa yă kakkaɓe, kyansa kuma yă lalace. Haka ma mai arziki zai shuɗe yayinda yake cikin harkarsa.

  23. Yaƙub 1:12kusan 60 M.

    Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.

  24. Yaƙub 1:13kusan 60 M.

    Sa’ad da aka jarrabci mutum, kada yă ce, “Allah ne yake jarrabtarsa.” Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa;

  25. Yaƙub 1:14kusan 60 M.

    amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi.