Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Yaƙub 1:15kusan 60 M.

    Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa.

  2. Yaƙub 1:16kusan 60 M.

    Kada a ruɗe ku, ’yan’uwana ƙaunatattu.

  3. Yaƙub 1:17kusan 60 M.

    Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

  4. Yaƙub 1:18kusan 60 M.

    Ya zaɓa yă haife mu ta wurin kalmar gaskiya, domin mu zama ’ya’yan fari na dukan abin da ya halitta.

  5. Yaƙub 1:19kusan 60 M.

    ’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,

  6. Yaƙub 1:20kusan 60 M.

    gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so.

  7. Yaƙub 1:21kusan 60 M.

    Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi na’am da maganar da aka shuka a cikinku da tawali’u, wadda za tă iya cetonku.

  8. Yaƙub 1:22kusan 60 M.

    Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce.

  9. Yaƙub 1:23kusan 60 M.

    Duk wanda yake ji magana ne kawai, bai kuwa aikata abin da ta ce ba, yana kama da mutumin da ya kalli fuskarsa a madubi

  10. Yaƙub 1:24kusan 60 M.

    bayan ya kalli kansa, sa’ad da ya tashi daga wurin, nan da nan sai yă manta da kamanninsa.

  11. Yaƙub 1:25kusan 60 M.

    Amma duk mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yă mance ba, sai dai mai yi ne yă zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi.

  12. Yaƙub 1:26kusan 60 M.

    In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne.

  13. Yaƙub 1:27kusan 60 M.

    Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.

  14. Yaƙub 2:1kusan 60 M.

    ’Yan’uwana, a matsayinmu cikin Ubangiji Yesu Kiristi maɗaukaki, kada ku nuna bambanci.

  15. Yaƙub 2:2kusan 60 M.

    A ce wani ya shigo cikin taronku saye da zoben zinariya da riguna masu tsada, wani matalauci kuma saye da tsummoki shi ma ya shigo,

  16. Yaƙub 2:3kusan 60 M.

    in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,”

  17. Yaƙub 2:4kusan 60 M.

    ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ke nan ba, kuka kuma zama alƙalai masu mugayen tunani?

  18. Yaƙub 2:5kusan 60 M.

    Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?

  19. Yaƙub 2:6kusan 60 M.

    Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu?

  20. Yaƙub 2:7kusan 60 M.

    Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba?

  21. Yaƙub 2:8kusan 60 M.

    In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.

  22. Yaƙub 2:9kusan 60 M.

    Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka.

  23. Yaƙub 2:10kusan 60 M.

    Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan.

  24. Yaƙub 2:11kusan 60 M.

    Gama shi da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan.

  25. Yaƙub 2:12kusan 60 M.

    Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da ’yanci,