Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Masu tawali’u za su sāke yin farin ciki a cikin Ubangiji; mabukata za su yi farin ciki cikin Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  2. Saboda haka ga abin da Ubangiji wanda ya fanshi Ibrahim, ya ce wa gidan Yaƙub, “Ba za a ƙara kunyata Yaƙub ba; fuskokinsu kuma ba za su ƙara yanƙwanewa ba.

  3. Sa’ad da suka ga ’ya’yansu a tsakiyarsu, aikin hannuwansu, za su kiyaye sunana da tsarki; za su san tsarkin Mai Tsarkin nan na Yaƙub, za su kuma ji tsoron Allah na Isra’ila.

  4. “Kaiton ’ya’ya masu tayarwa,” in ji Ubangiji, “ga waɗanda suke ƙulle-ƙullen da ba nawa ba, suna yin yarjejjeniya, amma ba ta Ruhuna ba, suna jibga zunubi a kan zunubi;

  5. waɗanda suka gangara zuwa Masar ba tare da sun nemi shawarata; waɗanda suke neman taimakon kāriyar Fir’auna, don neman inuwar mafakar Masar.

  6. Waɗannan mutane masu tawaye, ’ya’ya masu ruɗu, ’ya’yan da ba sa niyya su saurara ga umarnan Ubangiji.

  7. Ku bar wannan hanya, ku tashi daga wannan hanya, ku kuma daina kalubalantarmu da Mai Tsarkin nan na Isra’ila!”

  8. Saboda haka, ga abin da Mai Tsarkin nan na Isra’ila yake cewa, “Saboda haka kun ƙi wannan saƙo, kuka dogara ga aikin kama-karya kuka kuma dogara ga yin ruɗu,

  9. Zai rushe kucu-kucu kamar tukunyar yumɓu, ya ragargaje ƙaf har cikin gutsattsarinsa ba za a sami ko ɗan katanga don ɗiba garwashin wuta ko a ɗiba ruwa daga tanki ba.”

  10. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa, “Cikin tuba da hutu ne kaɗai cetonku yake, cikin shiru da dogara gare ni ne za ku sami ƙarfinku, amma ba za ku sami ko ɗaya a cikinsu ba.

  11. Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri; ya tashi don yă nuna muku jinƙai. Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya. Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!

  12. Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku.

  13. Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su.

  14. Zai kuma aiko muku da ruwan sama don shuki a ƙasa, kuma abincin da zai fito daga gona zai zama mai albarka da kuma mai yawa. A wannan rana shanu za su yi kiwo a wadatacciyar makiyaya.

  15. Wata zai yi haske kamar rana, kuma hasken rana zai ma yi sau bakwai na haskenta, kamar hasken cikakku ranaku bakwai, sa’ad da Ubangiji zai ɗaura raunukan mutanensa ya kuma warkar da raunukan da ya yi musu.

  16. Duba, Sunan Ubangiji yana zuwa daga nesa, tare da fushi mai ƙuna da kuma baƙin hayaƙi; leɓunansa sun cika da fushi, harshensa kuma wuta ce mai cinyewa.

  17. Numfashinsa kamar raƙuman ruwa masu gudu yana tashi har zuwa wuya. Yakan tankaɗe al’ummai cikin lariyar hallaka; yakan sa a muƙamuƙan mutane linzamin da zai jagorance su su kauce.

  18. Za ku kuma rera kamar a daren da kuke shagalin biki mai tsarki; zukatanku za su yi farin ciki kamar sa’ad da mutane sukan haura da busa zuwa dutsen Ubangiji, zuwa Dutse na Isra’ila.

  19. Ubangiji zai sa mutane su ji muryarsa mai daraja ya kuma sa su ga hannunsa na saukowa tare da fushi mai ƙuna da kuma wuta mai cinyewa, gizagizai za su ɓarke, za a yi hadarin tsawa da ƙanƙara.

  20. Muryar Ubangiji za tă firgita Assuriya da sandar mulkinsa zai kashe su.

  21. Kowane bugun da Ubangiji zai yi musu da bulalarsa na hukunci zai zama kiɗi ga ganguna da garaya, yayinda yake yaƙi da su da naushin hannunsa.

  22. An riga an shirya wurin ƙonawa; an shirya shi saboda sarki. An haƙa ramin wutarsa da zurfi da kuma fāɗi, da isashen wuta da itacen wuta; numfashin Ubangiji, yana kamar kibiritu mai ƙuna, da aka sa masa wuta.

  23. Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako, waɗanda suke dogara ga dawakai, waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu, amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila, ko ya nemi taimako daga Ubangiji.

  24. Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa; ba ya janye kalmominsa. Zai yi gāba da gidan mugu, gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta.

  25. Amma Masarawa mutane ne ba Allah ba; dawakansu nama da jini ne ba ruhu ba. Sa’ad da Ubangiji ya miƙa hannunsa, shi da yake taimako zai yi tuntuɓe shi da aka taimaka zai fāɗi; dukansu biyu za su hallaka tare.