God
Ayoyin da suka ambaci God
A wannan dutse zai kawar da baƙin cikin da ya lulluɓe dukan mutane, ƙyallen da ya rufe dukan al’ummai;
zai haɗiye mutuwa har abada. Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye daga dukan fuskoki; zai kawar da kunyar mutanensa daga dukan duniya. Ubangiji ne ya faɗa.
A wannan rana za su ce, “Tabbatacce wannan shi ne Allah; mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu. Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi; bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.”
Hannun Ubangiji zai zauna a kan wannan dutse; amma za a tattake Mowab a ƙarƙashinsa kamar yadda ake tattaka kara a cikin taki.
Za su buɗe hannuwansa a cikinsa, yadda mai iyo kan buɗe hannuwansa don yă yi iyo. Allah ya ƙasƙantar da girmankansu duk da wayon hannuwansu.
Zai rurrushe manyan katangar kagaru ya kuma ƙasƙantar da su; zai rushe su har ƙasa, su zama ƙura.
A wannan rana za a rera wannan waƙa a ƙasar Yahuda. Muna da birni mai ƙarfi; Allah yake ceton katanga da kuma kagarunta.
Za ka kiyaye shi da cikakken salama shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka, domin ya dogara a gare ka.
Ku dogara ga Ubangiji, gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.
Yakan ƙasƙantar da waɗanda suke zama a bisa ya kawar da birni mai alfarma ƙasa; ya rusa ta har ƙasa ya jefar da ita cikin ƙura.
Hanyar masu adalci sumul take; Ya Mai Aikata Gaskiya, ka sa hanyar masu adalci ta yi sumul.
I, Ubangiji, cikin tafiya a hanyar dokokinka, muna sa zuciya gare ka; sunanka da tunani a kanka su ne marmarin zukatanmu.
Raina yana marmarinka da dare; da safe kuma raina yana son ganinka. Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya, mutanen duniya kan koyi adalci.
Ko da yake akan nuna wa mugaye alheri, ba sa koyi adalci; har ma a ƙasar masu aikata gaskiya sukan ci gaba da aikata mugunta ba sa ganin girmar darajar Ubangiji.
Ya Ubangiji an ɗaga hannunka sama, amma ba sa ganinsa. Bari su ga himmarka don mutanenka su kuma sha kunya; bari wutar da aka ajiye don abokan gābanka ta cinye su.
Ubangiji ka kafa salama dominmu; duk abin da muka iya yi kai ne ka yi mana.
Ya Ubangiji, Allahnmu, waɗansu iyayengiji ban da kai sun yi mulki a kanmu, amma sunanka kaɗai muka girmama.
Yanzu duk sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba; waɗannan ruhohin da suka rasu ba za su tashi ba. Ka hukunta su ka kuma kawo su ga hallaka; ka sa ba za a ƙara tunawa da su ba.
Ka fadada al’umma, ya Ubangiji; ka fadada al’umma. Ka samo wa kanka ɗaukaka; ka fadada dukan iyakokin ƙasar.
Ubangiji, sun zo gare ka a cikin damuwarsu; sa’ad da ka hore su, da ƙyar suna iya yin addu’a.
Kamar mace mai ciki da take gab da haihuwa takan yi ta murɗawa tana kuka saboda zafi, haka muka kasance a gabanka, ya Ubangiji.
Ku tafi, mutanena, ku shiga ɗakunanku ku kuma kulle ƙofofi; ku ɓoye kanku na ɗan lokaci sai ya huce fushinsa.
Duba, Ubangiji yana fitowa daga mazauninsa don yă hukunta mutanen duniya saboda zunubansu. Duniya za tă bayyana zub da jinin da aka yi a kanta; ba za tă ƙara ɓoye waɗanda aka kashe a cikinta ba.
A wannan rana, Ubangiji zai yi hukunci da takobi, takobinsa mai tsanani, mai ƙarfi da kuma mai muguwar ɓarna, zai hukunta dodon ruwa macijin nan da ya kanannaɗe, dodon ruwa macijin nan mai murɗewa; zai kashe dodon nan na teku.
Ni, Ubangiji na lura da ita; na yi ta yin mata banruwa. Na yi tsaronta dare da rana don kada wani yă yi mata ɓarna.