Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. ‘Ga abin da Ubangiji ya ce zai kawo masifa a wannan wuri da mutanensa, dukan la’anar da aka rubuta a cikin littafin da aka karanta a gaban sarkin Yahuda.

  2. Domin sun yashe ni suka kuma ƙone turare wa waɗansu alloli, suka tsokane ni in yi fushi ta wurin dukan abin da hannuwansu suka yi, fushina zai zuba a kan wannan wuri, ba kuma za a kwantar da shi ba.’

  3. Ku faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aike ku ku nemi nufin Ubangiji, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yake cewa game da kalmomin da ka ji.

  4. Domin zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah sa’ad da ka ji abin da ya yi magana a kan wannan wuri da mutanensa, domin kuma ka ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yage rigunanka ka kuma yi kuka a gabana, na ji ka, in ji Ubangiji.

  5. Yanzu zan tara ka da kakanninka, za a kuma binne ka cikin salama. Idanunka ba za su ga dukan masifar da zan kawo a kan wannan wuri da kuma a kan waɗanda suke zama a nan ba.’ ” Sai suka kai amsar wa sarki.

  6. Ya haura zuwa haikalin Ubangiji tare da mutanen Yahuda, mutanen Urushalima, firistoci da Lawiyawa, dukan mutane daga ƙarami zuwa babba. Ya karanta dukan kalmomin Littafin Alkawari wanda aka samu a cikin haikalin Ubangiji a kunnuwansu.

  7. Sai sarkin ya miƙe tsaye a inda yake, ya sabunta alkawari a gaban Ubangiji, don yă bi Ubangiji yă kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa da kuma farillansa da dukan zuciyarsa da kuma dukan ransa, ya kuma yi biyayya da kalmomin alkawarin da aka rubuta a cikin wannan littafi.

  8. Sa’an nan ya sa kowa a Urushalima da Benyamin ya yi alkawari ga wannan; mutanen Urushalima suka aikata wannan bisa ga alkawarin Allah, Allah na kakanninsu.

  9. Yosiya ya fitar da dukan gumakan banƙyama daga dukan yankunan Isra’ilawa, ya kuma sa dukan waɗanda suke a Isra’ila su bauta wa Ubangiji Allahnsu. Muddin ransa, ba su fasa bin Ubangiji Allah na kakanninsu ba.

  10. Yosiya ya yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji a Urushalima, aka kuma yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a ranar goma sha huɗu ga wata na farko.

  11. Ya zaɓi firistoci su yi aikinsu, sai ya ƙarfafa su su yi aikin da kyau a hidimar haikalin Ubangiji.

  12. Ya ce wa Lawiyawa waɗanda suke koyar da dukan Isra’ila da kuma waɗanda aka tsarkake wa Ubangiji. “Ku sa akwatin alkawari mai tsarki a cikin haikalin da Solomon ɗan Dawuda sarkin Isra’ila ya gina. Ba za a riƙa ɗaukansa a kafaɗa ba. Yanzu ku bauta wa Ubangiji Allahnku da kuma mutanensa Isra’ila.

  13. Ku yanka ragunan Bikin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku kuma shirya raguna domin ’yan’uwanku, kuna yin abin da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.”

  14. Fadawansa su ma suka ba da taimako da yardar rai ga mutane da kuma firistoci da Lawiyawa. Hilkiya, Zakariya da Yehiyel masu aiki a haikalin Allah, suka ba firistoci hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyu da ɗari shida da kuma shanu ɗari uku.

  15. Suka keɓe hadayun ƙonawa don su ba da su ga ƙungiyoyin iyalan mutane don su miƙa ga Ubangiji, yadda yake a rubuce a Littafin Musa. Suka yi haka da shanun.

  16. Ta haka fa aka yi dukan hidimar Ubangiji a wannan rana, domin su kiyaye Bikin Ƙetarewa, domin kuma su miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji, yadda sarki Yosiya ya umarta.

  17. Amma Neko ya aiki ’yan saƙo ga Yosiya, yana cewa, “Me ya gama ni da kai, ya Sarkin Yahuda? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da gidan da yake gāba da ni! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada yă hallaka ka.”

  18. Yosiya fa, bai juya daga gare shi ba, amma ya ɓad da kama don yă yi yaƙin. Bai saurari abin da Neko ya faɗa bisa ga umarnin Allah ba, amma ya tafi ya yaƙe shi a filin Megiddo.

  19. Sauran ayyukan mulkin Yosiya da kuma kyawawan abubuwan da ya yi, bisa ga abin da aka rubuta a Dokar Ubangiji,

  20. Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa.

  21. Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kuma kwaso kayayyaki daga haikalin Ubangiji ya sa su a haikalinsa a can.

  22. Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji.

  23. Da bazara, Sarki Nebukadnezzar ya aika a kawo Yehohiyacin, aka kuma kawo shi Babilon, tare da kayayyaki masu daraja daga haikalin Ubangiji, sai Sarki Nebukadnezzar ya naɗa kawunsa Zedekiya, sarki a bisa Yahuda da Urushalima.

  24. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa kuma bai ƙasƙantar da kansa a gaban Irmiya annabi, wanda ya yi magana kalmar Ubangiji ba.

  25. Ya tayar wa Sarki Nebukadnezzar, wanda ya sa ya yi rantsuwa da sunan Allah. Ya zama mai kunnen ƙashi da kuma taurin zuciya, bai kuwa juye ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ba.