Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Bugu da ƙari, dukan shugabannin firistoci da mutane suka ƙara zama marasa aminci, suna bin dukan abubuwan banƙyama na al’ummai, suka ƙazantar da haikalin Ubangiji, wanda ya tsarkake a Urushalima.

  2. Sai Ubangiji Allah na kakanninsu, ya yi ta aika da magana gare su ta wurin ’yan saƙonsa sau da sau, domin ya ji tausayi mutanensa da mazauninsa.

  3. Amma suka yi wa ’yan saƙon Allah ba’a, suka rena maganarsa, suka yi wa annabawansa dariyar reni, har sai da fushin Ubangiji ya tasar a kan mutanensa babu makawa.

  4. Ya bashe su ga sarkin Babiloniyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a wuri mai tsarki, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka ga Nebukadnezzar.

  5. Nebukadnezzar ya kwashe dukan kayayyaki daga haikalin Allah, babba da ƙarami, da ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin sarki da na fadawansa zuwa Babilon.

  6. Suka cinna wa haikalin Allah wuta, suka rurrushe katangar Urushalima; suka ƙone dukan fada, suka kuma lalace kome mai amfani da yake can.

  7. Ƙasar ta more hutun Asabbacinta; a dukan lokacin zamanta kango ta huta, har sai da shekaru saba’in nan suka cika bisa ga maganar Ubangiji da Irmiya ya faɗi.

  8. Don a cika maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya, a shekara farko ta Sairus sarkin Farisa, sai Ubangiji ya motsa zuciyar Sairus na Farisa don yă yi shela a dukan masarautarsa, ya kuma sa shi a rubuce cewa,

  9. “Ga abin da Sairus sarkin Farisa ya ce, “ ‘Ubangiji Allah na sama, ya ba ni dukan mulkokin duniya, ya kuma naɗa ni in gina masa haikali a Urushalima a Yahuda. Duk wani na mutanensa a cikinku, bari yă haura yă tafi, bari kuma Ubangiji Allahnsa yă kasance tare da shi.’ ”

  10. A shekara ta farko ta mulkin sarkin Farisa, wato, sarki Sairus, domin a cika maganar Ubangiji da aka yi ta bakin Irmiya, sai Ubangiji ya taɓa zuciyar Sairus sarkin Farisa ya yi shela a duk fāɗin ƙasarsa, ya kuma rubuta cewa,

  11. “Ga abin da Sairus sarkin Farisa yake shela, “ ‘Ubangiji Allah na sama ya ba ni iko in yi mulkin duniya duka, ya kuma zaɓe ni in gina masa haikali a Urushalima cikin Yahuda.

  12. Duk wanda yake nasa a cikinku bari Allahnsa yă kasance tare da shi, bari yă tafi Urushalima cikin Yahuda yă gina haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila, Allah wanda yake a Urushalima.

  13. Duk inda akwai mutumin Yahuda da ya rage, sai mutanen da suke zama kusa da shi, su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da kuma dabbobi, tare da kyautai na yardar rai saboda Gidan Allah wanda yake a Urushalima.’ ”

  14. Sai shugabannin zuriyar Yahuda da na Benyamin, da firistoci da Lawiyawa, duk wanda Allah ya taɓa zuciyarsa, suka shirya don su je su gina haikalin Ubangiji a Urushalima.

  15. Sai sarki Sairus ya fitar da kayan da suke na haikalin Ubangiji waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga Urushalima ya sa a haikalin allahnsa.

  16. Sa’ad da suka isa haikalin Ubangiji a Urushalima, sai waɗansu shugabannin iyalai suka yi bayarwar yardar rai ta gudummawarsu domin sāke gina gidan Allah a wurin da yake.

  17. Sai Yeshuwa ɗan Yozadak da sauran firistoci, da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da abokan aikinsa, suka fara gina bagaden Allah na Isra’ila don miƙa hadaya ta ƙonawa bisa ga abin da yake a rubuce a Dokar Musa mutumin Allah.

  18. Duk da tsoron da suke ji na mutanen da suke kewaye da su, sun gina bagaden a wurinsa, suka kuma miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagaden ga Ubangiji safe da yamma.

  19. Bayan wannan, suka miƙa hadayu na ƙonawa yadda aka saba. Suka miƙa hadayu na Sabon Wata, da hadayu na bukukkuwan Ubangiji, da kuma hadayun da aka bayar da yardar rai ga Ubangiji.

  20. A ranar farko ta watan bakwai, sai suka fara miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko da yake ba a riga an aza harsashin ginin haikalin Ubangiji ba.

  21. A wata na biyu na shekara ta biyu, bayan sun komo gidan Allah a Urushalima, sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, Yoshuwa ɗan Yozadak da sauran ’yan’uwansa (Firistoci da Lawiyawa da duk waɗanda suka komo Urushalima daga bauta) suka fara aiki, aka zaɓi Lawiyawa daga masu shekaru ashirin da haihuwa zuwa waɗanda suka wuce haka don su dubi aikin ginin gidan Ubangiji.

  22. Yeshuwa da ’ya’yansa maza, da ’yan’uwansa, da Kadmiyel da ’ya’yan Yahuda (’yan zuriyar Hodawiya), da ’ya’yan Henadad, da ’ya’yansu da ’yan’uwansu, dukansu Lawiyawa ne, suka haɗa kai cikin duban masu aikin gidan Allah.

  23. Da masu ginin suka aza harsashin ginin haikalin Ubangiji, sai firistoci suka sa kayansu na firistoci suka riƙe ƙahonin busa, Lawiyawa (’ya’yan Asaf) kuwa suka riƙe kuge, suka yi shiri domin su rera yabo ga Ubangiji kamar yadda Dawuda Sarkin Isra’ila ya ba da umarni.

  24. Suka rera waƙar yabo da godiya ga Ubangiji, suna cewa, “Shi nagari ne; ƙaunarsa kuwa ga Isra’ila har abada ce.” Dukan jama’a kuwa suka yabi Ubangiji da murya mai ƙarfi, domin an aza harsashin ginin gidan Ubangiji.

  25. Sa’ad da abokan gāban Yahuda da na Benyamin suka ji cewa waɗanda suka dawo daga bauta suna gina haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila