Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wicked

724 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yakan ragargaza waɗanda suka shiga hannu, su fāɗi; sukan fāɗi a ƙarƙashin ƙarfinsa.

  2. Yakan ce wa kansa, “Ai, Allah ya manta; ya rufe fuskarsa ba ya gani.”

  3. Ubangiji yana bincike adalai, amma ransa yana ƙi mugaye da masu son rikici.

  4. Ya Ubangiji, da hannunka ka cece ni daga irin mutanen nan, daga mutanen duniyan nan waɗanda ladarsu yana a wannan rayuwa ne. Kakan cika yunwan waɗanda kake so; ’ya’yansu suna da isashe suna kuma ajiyar wadata wa ’ya’yansu.

  5. Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka; sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka.

  6. Sun nemi taimako, amma ba su sami wanda zai cece su ba, ga Ubangiji, amma bai amsa ba.

  7. Azaban mugu da yawa suke, amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa kan kewaye mutumin da ya dogara gare shi.

  8. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Akwai magana a cikin zuciyata game da zunubin mugu. Babu tsoron Allah a idanunsa.

  9. Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa.

  10. Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu; ya daina zama mai hikima da yin alheri.

  11. Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta; yakan sa kansa ga aikata zunubi kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau.

  12. Ta Dawuda. Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;

  13. Mugaye sukan shirya wa adalai maƙarƙashiya su ciji baki a kansu;

  14. gama za a kakkarya ikon mugaye, amma Ubangiji zai riƙe mai adalci.

  15. Kwanakin marasa zarge suna sane ga Ubangiji, kuma gādonsu zai dawwama har abada.

  16. A lokutan masifu ba za su yanƙwane ba; a kwanakin yunwa za su sami a yalwace.

  17. Amma mugaye za su hallaka, Abokan gāban Ubangiji za su zama kamar kyan gonaki, za su ɓace, za su ɓace kamar hayaƙi.

  18. Mugaye kan yi rance ba sa kuma biya, amma masu adalci suna bayar hannu sake;

  19. waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka za su gāji ƙasar, amma waɗanda ya la’anta, za a kore su.

  20. Na ga wani mugu, azzalumi, yana yaɗuwa kamar ɗanyen itace a asalin ƙasarsa,

  21. amma yakan mutu nan da nan kuma ba ya ƙara kasancewa; ko an neme shi, ba za a same shi ba.

  22. Ka dubi marasa zargi, ka lura da adali; akwai sa zuciya domin mutum mai salama.

  23. Amma za a hallaka dukan masu zunubi; za a yanke sa zuciya ta mugaye.

  24. Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu.

  25. Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.