Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wicked

724 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ko Allah yana sauraron kukansa lokacin da ƙunci ya auko masa?

  2. “Ga abin da mugaye za su samu gādon da azzalumi zai samu daga Maɗaukaki.

  3. Kome yawan ’ya’yansa, takobi za tă gama da su; zuriyarsa ba za su taɓa samun isashen abinci ba.

  4. Waɗanda suka tsira annoba za tă kashe su, kuma gwaurayensu ba za su yi kukan mutuwarsu ba.

  5. Ko da yake ya tara azurfa kamar ƙasa, tufafi kuma kamar tarin ƙasa,

  6. abin da ya tara masu adalci za su sa marasa laifi za su raba azurfarsa.

  7. Gidan da ya gina kamar gidan gizo-gizo, kamar bukkar mai tsaro.

  8. Attajiri zai kwanta, amma daga wannan shi ke nan; lokacin da zai buɗe idanunsa, kome ya tafi.

  9. Tsoro zai kwashe shi kamar ambaliyar ruwa; Da dare iska za tă tafi da shi.

  10. Iskar gabas za tă tafi da shi; shi ke nan ya ƙare; za tă share shi daga wurinsa.

  11. Za tă murɗe shi ba tausayi, lokacin da yake guje wa ikon iskar.

  12. Zai tafa hannu yă yi tsaki yă kawar da shi daga wurinsa.”

  13. Gama Allah yana magana, yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya ko da yake ba lalle mutum yă lura ba.

  14. A cikin mafarki, cikin wahayi da dare, sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane lokacin da suke cikin barci kan gadajensu,

  15. mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu yă razana su da gargaɗinsa,

  16. don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba a kuma hana su daga girman kai,

  17. don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami, a kāre su daga hallaka ta wurin takobi.

  18. “Ko kuma mutum yă sha horo ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa,

  19. yadda zai ji ƙyamar abinci, har yă ƙi son abinci mafi daɗi.

  20. Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito.

  21. Ransa yana matsawa kusa da rami, ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa.

  22. Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci, ɗaya daga cikin dubu, da zai gaya wa mutum abin da yake daidai gare shi,

  23. yă yi masa alheri yă ce, ‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami, na samu fansa dominsa.’

  24. Sa’an nan fatar jikinsa za tă zama sabuwa kamar ta jariri; za tă zama kamar lokacin da yake matashi.

  25. Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa, yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna; Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci.