Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wicked

724 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce, ‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai, amma ban samu abin da ya kamata in samu ba.

  2. Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami, kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’

  3. “Allah ya yi wa mutum duk waɗannan, sau biyu, har ma sau uku.

  4. Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami, don hasken rai ya haskaka a kansa.

  5. Ba ya amsawa lokacin da mutane suka yi kira don taimako domin girman kan mugaye.

  6. Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi; Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu.

  7. Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a.

  8. Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana.

  9. Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.

  10. Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa.

  11. Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba, balle a sami masu zunubi a taron adalai.

  12. Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.

  13. Masu fariya ba za su iya tsaya a gabanka ba. Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba.

  14. Kakan hallaka masu yin ƙarya. Masu kisankai da mutane masu ruɗu Ubangiji yana ƙyama.

  15. Babu ko kalma guda daga bakinsu da za a dogara da ita; marmarinsu kawai shi ne su hallakar da waɗansu. Maƙogwaronsu buɗaɗɗen kabari ne; da harshensu suna faɗin ƙarya.

  16. Allah alƙali ne mai adalci, Allahn da yakan bayyana fushinsa kowace rana.

  17. Wanda yake da cikin mugunta ya kuma ɗauki cikin damuwa yakan haifi ƙarya.

  18. Wanda ya haƙa rami yakan fāɗa cikin ramin da ya haƙa.

  19. Damuwar da ya ja yakan sāke nannaɗe a kansa; fitinarsa takan sauka a kansa.

  20. Cikin ɗaga kai mutum ba ya neman Allah; cikin tunaninsa ba ya ba da wata dama saboda Allah.

  21. Hanyoyinsa kullum sukan yi nasara; yana da girman kai kuma dokokinka suna nesa da shi; yakan yi wa dukan abokan gābansa duban reni.

  22. Yakan ce wa kansa, “Ba abin da zai girgiza ni; kullum zan yi murna ba zan taɓa shiga wahala ba.”

  23. Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana; wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa.

  24. Yakan yi kwanto kusa da ƙauyuka; daga kwanton yakan kashe marar laifi. Yana kallon waɗanda za su shiga hannunsa a ɓoye.

  25. Yakan yi kwanto a ɓoye kamar zaki. Yakan yi kwanto don yă kama marasa ƙarfi; yakan kama marasa ƙarfi yă ja su cikin ragarsa.