Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Unity of God

46 ayoyi · 20 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku tuna da abubuwan da suka riga suka faru, waɗannan na tun dā; ni ne Allah, kuma babu wani; ni ne Allah kuma babu wani kamar ni.

  2. Nakan sanar da ƙarshe tun daga farko, daga fil azal, abin da yake zuwa nan gaba. Na ce nufina zai tabbata, kuma zan aikata dukan abin da na gan dama.

  3. Daga gabas na kira tsuntsun da yake farauta; daga can ƙasa mai nesa, wani mutumin da zai cika nufina. Abin da na riga na faɗa, shi zan sa ya faru; abin da na shirya, shi zan aikata.

  4. Wane ne Allah kamar ka, wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu? Ba ka zama mai fushi har abada amma kana marmari ka nuna jinƙai.

  5. Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’”

  6. Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”

  7. “Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”

  8. Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan. ‘Ku saurara, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.

  9. Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’

  10. Da ni da Uba ɗaya ne.”

  11. Yesu ya amsa ya ce, “Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’?

  12. Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa.

  13. Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu.

  14. Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko.

  15. To, game da cin abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa, mun san cewa “Gunki ba kome ba ne a duniya”, kuma “Babu wani Allah sai dai ɗaya.”

  16. duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.

  17. Allah ɗaya Uban duka, wanda yake a bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma.

  18. Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu,

  19. Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki.

  20. Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce?

  21. Akwai shaidu uku, wato,