Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Unity of God

46 ayoyi · 20 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku bincika dukan tarihi mana, tun daga lokacin da Allah ya halicci mutane a cikin duniya har yă zuwa yanzu; ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa?

  2. Akwai waɗansu mutanen da suka taɓa jin muryar Allah yana magana daga wuta, kamar yadda kuka ji har suka rayu?

  3. Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku?

  4. An nuna muku dukan waɗannan abubuwa saboda ku san cewa Ubangiji, shi ne Allah; ban da shi, babu wani.

  5. Ku sani, ku kuma riƙe a zuciya a wannan rana, cewa Ubangiji shi ne Allah a sama da kuma a ƙasa. Babu wani kuma.

  6. Ku kiyaye ƙa’idodi da umarnai, waɗanda nake ba ku a yau, domin zaman lafiyarku da kuma na zuriyarku bayan ba ku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.

  7. Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.

  8. Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku.

  9. “Ku duba yanzu cewa ni ne Shi! Ba wani allah in ban da ni. Nakan kashe in kuma rayar, nakan sa rauni in kuma warkar, ba wanda yake da iko yă cece wani daga hannuna.

  10. “Kai mai girma ne, ya Ubangiji Mai Iko Duka! Babu wani kamar ka, babu kuma wani Allah sai kai; kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.

  11. Hezekiya kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda yake zaune tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah bisa dukan mulkokin duniya. Kai ka yi sama da duniya.

  12. “Babu wani kamar ka, ya Ubangiji, babu kuma Allah sai kai, kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.

  13. Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.

  14. Bari su san cewa kai, wanda sunansa ne Ubangiji, cewa kai kaɗai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya.

  15. Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki; kai kaɗai ne Allah.

  16. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, Sarki da kuma Mai Fansar Isra’ila, Ubangiji Maɗaukaki. Ni ne farko ni ne kuma ƙarshe; in ban da ni babu wani Allah.

  17. Kada ku firgita kada kuma ku ji tsoro. Ban furta wannan na kuma yi faɗar haka tuntuni ba? Ku ne shaiduna. Akwai wani Allah in ban da ni? A’a, babu wani Dutse; ban san da wani ba.”

  18. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarka, wanda ya yi ka a cikin mahaifa. “Ni ne Ubangiji, wanda ya yi dukan abubuwa, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya da kansa,

  19. Ni ne Ubangiji, kuma babu wani; in ban da ni babu wani Allah. Zan ƙarfafa ka, ko da yake ba ka san ni ba,

  20. saboda daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta mutane za su san cewa babu wani in ban da ni. Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.

  21. Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu, ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i; ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.

  22. “Ku sammai, ku sauko da adalci kamar ruwan sama; bari gizagizai su zubar da yayyafi kamar adalci. Bari ƙasa ta buɗe, bari ceto ya tsiro, bari adalci ya yi girma tare da shi; ni, Ubangijine, na sa ya faru.

  23. Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci sammai, shi ne Allah; shi da ya sarrafa ya kuma yi duniya, ya kafa ta; bai halicce ta don ta zama ba kome ba, amma ya yi ta don a zauna a ciki, ya ce, “Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.

  24. Furta abin da zai kasance, ku gabatar da shi, bari su yi shawara tare. Wa ya faɗa wannan tuntuni, wa ya yi shelar sa a kwanakin dā? Ba ni ba ne, Ubangiji? Kuma babu Allah in ban da ni, Allah mai adalci da kuma Mai Ceto; babu wani sai ni.

  25. “Ku juyo gare ni ku sami ceto, dukanku iyakokin duniya; gama ni ne Allah, kuma babu wani.