Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Sidonians

54 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. da kuma dukan sarakunan arewa, nesa da kuma kusa, bi da bi, dukan mulkokin duniya. Bayan dukansu kuma, sai sarkin Sheshak ma yă sha.

  2. “Sa’an nan na faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku sha, ku bugu ku kuma yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku ƙara tashi saboda takobin da zan aiko muku.’

  3. Amma in suka ki su karɓi kwaf ɗin daga hannunka su sha, ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa dole ku sha!

  4. Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.

  5. Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa.

  6. Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’

  7. Gama rana ta zo da za a hallaka Filistiyawa a kuma datse dukan waɗanda suka ragu waɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon. Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa, raguwa daga bakin tekun Kaftor.

  8. Mutanen Sidon da Arfad su ne matuƙan jirgin ruwanki; gwanayenki, ya Taya, suna ciki a matsayi matuƙan jiragen ruwa.

  9. “ ‘Yahuda da Isra’ila sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki da alkama da Minnit da alawa, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.

  10. “Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon; ka yi annabci a kanta

  11. ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ina gāba da ke, ya Sidon, zan sami ɗaukaka a cikinki. Za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na zartar da hukunci a kanta na kuma nuna kaina mai tsarki a cikinta.

  12. Zan aika da annoba a kanta in kuma sa jini ya zuba a titunanta. Kisassu za su fāɗi a cikinta, da takobi yana gāba da ita a kowane gefe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.

  13. “ ‘Mutanen Isra’ila ba za su ƙara kasance da mugayen maƙwabta waɗanda za su zama sarƙaƙƙiya masu zafi da ƙaya mai tsini ba. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.

  14. Za su fāɗi cikin waɗanda aka kashe da takobi. Takobin da an zāre; bari a ja ta a tafi tare da dukan jama’arta.

  15. “Yanzu mene ne damuwarku da ni, ya Taya da Sidon da kuma dukan mazaunan yankunan Filistiya? Kuna ƙoƙari ku sāka mini don abin da na yi ne? In kuna sāka mini ne, to, da gaggawa zan mayar muku da sakayya a kanku.

  16. Gama kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe dukiyata mafi kyau kun kai cikin haikalinku.

  17. Kun sayar da mutanen Yahuda da na Urushalima ga mutanen Hellenawa, don ku aika da su nesa da ƙasarsu.

  18. Zan sayar da ’ya’yanku maza da mata ga mutanen Yahuda, su kuma za su sayar da su ga mutanen Sabenawa, al’umma da take nesa da ku.” Ubangiji ya faɗa.

  19. “Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka.

  20. Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku.

  21. Barin wurin ke nan, sai Yesu ya janye zuwa yankin Taya da Sidon.

  22. Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.”

  23. Mutane da yawa daga Yahudiya, da Urushalima, da Edom, da kuma yankunan da suke ƙetaren Urdun, da kewayen Taya, da Sidon suka zo wurinsa, don sun ji dukan abubuwan da yake yi.

  24. Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yă sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba.

  25. Macen kuwa mutuniyar Hellenawa ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yă fitar da aljani da yake jikin diyarta.