Skip to content

Ashtoreth

3 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Ashtoreth

  1. Ya bi Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa.

  2. Zan yi wannan domin sun yashe ni, suka kuma yi wa Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Kemosh, allahn Mowabawa, da kuma Molek, allahn Ammonawa sujada, ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ba su kuwa yi abin da yake daidai a idanuna ba, ba su kiyaye farillaina da dokokina kamar yadda Dawuda, mahaifin Solomon ya yi ba.

  3. Sarkin kuma ya lalatar da masujadan kan tuddan da suke gabas da Urushalima, kudu da Tudun Hallaka, waɗanda Solomon sarkin Isra’ila ya gina don Ashtarot, ƙazantacciyar alliyar Sidoniyawa, da Kemosh ƙazantaccen allah na Mowab, da kuma Molek allahn banƙyama na mutanen Ammon.