Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Psalms

896 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.

  2. A wannan rana za ku ce, “Zan yabe ka, ya Ubangiji. Ko da yake a dā ka yi fushi da ni, amma yanzu ka daina fushi da ni ka kuwa ta’azantar da ni.

  3. Tabbatacce Allah shi ne mai cetona; zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba. Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.”

  4. Da farin ciki zan ɗebo ruwa daga rijiyoyin ceto.

  5. A wannan rana za ku ce, “Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai, a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.

  6. Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa; bari a sanar da wannan ga dukan duniya.

  7. Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”

  8. Rubutun Hezekiya sarkin Yahuda bayan ciwonsa da kuma warkarwarsa.

  9. Na ce, “Cikin tsakiyar rayuwata dole in bi ta ƙofofin mutuwa a kuma raba ni da sauran shekaruna?”

  10. Na ce, “Ba zan ƙara ganin Ubangiji ba, Ubangiji a ƙasa ta masu rai; ba zan ƙara ga wani mutum, ko in kasance tare da waɗanda suke zama a wannan duniya ba.

  11. Kamar tentin makiyayi an rushe gidana aka kuma ƙwace ta daga gare ni. Kamar mai saƙa, na nannaɗe rayuwata, ya kuma yanke ni daga sandar saƙa; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.

  12. Na yi jira da haƙuri har safiya, amma kamar zaki ya kakkarya ƙasusuwana duka; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.

  13. Na yi kuka kamar mashirare ko zalɓe, na yi kuka kamar kurciya mai makoki. Idanuna suka rasa ƙarfi yayinda na duba sammai. Na damu; Ya Ubangiji, ka taimake ni!”

  14. Amma me zan ce? Ya riga ya yi mini magana, shi kansa ne kuma ya aikata. Zan yi tafiya da tawali’u dukan kwanakina saboda wahalar raina.

  15. Ubangiji, ta waɗannan abubuwa ne mutane suke rayuwa; ruhuna kuma yana samun rai a cikinsu shi ma. Ka maido mini da lafiya ka kuma sa na rayu.

  16. Tabbatacce wannan kuwa saboda ribata ne cewa in sha irin wahalan nan. Cikin ƙaunarka ka kiyaye ni daga ramin hallaka; ka sa dukan zunubaina a bayanka.

  17. Gama kabari ba zai yabe ka ba, matattu ba za su rera yabonka ba; waɗanda suka gangara zuwa rami ba za su sa zuciya ga amincinka ba.

  18. Masu rai, masu rai, su suke yabonka, kamar yadda nake yi a yau; iyaye za su faɗa wa ’ya’yansu game da amincinka.

  19. Ubangiji zai cece ni, za mu kuma rera da kayan kiɗi masu tsirkiya dukan kwanakinmu a cikin haikalin Ubangiji.

  20. Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa!

  21. Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina?

  22. Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna.

  23. Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!”

  24. Sai Maryamu ta ce, “Raina yana ɗaukaka Ubangiji

  25. ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,