Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prisons

63 ayoyi · 44 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Maigidan Yusuf ya ɗauke shi ya sa a kurkuku, wurin da ake tsare ’yan kurkukun sarki. Amma yayinda Yusuf yake can a cikin kurkuku,

  2. Ubangiji ya kasance tare da shi; ya nuna masa alheri, ya kuma sa ya sami tagomashi a idanun mai gadin kurkukun.

  3. Saboda haka mai gadin ya sa Yusuf ya zama shugaban dukan waɗanda aka tsare a kurkukun, Yusuf ne kuma yake lura da dukan abin da ake yi a can.

  4. Mai gadin ba ya sa kansa game da kome da yake ƙarƙashin kulawar Yusuf, gama Ubangiji yana tare da Yusuf, ya kuma ba shi nasara a cikin dukan abin da ya yi.

  5. ya kuma sa su a kurkuku a cikin gidan shugaban masu tsaro, a wannan kurkukun da aka sa Yusuf.

  6. Ya mai da shugaban masu shayarwa a matsayinsa, saboda haka shugaban masu shayarwa ya sāke sa kwaf a hannun Fir’auna,

  7. amma ya rataye shugaban masu tuya, kamar dai yadda Yusuf ya faɗa musu a fassarar mafarkan da suka yi.

  8. In ku mutane masu gaskiya ne, ku bar ɗaya daga cikin ’yan’uwanku yă zauna a kurkuku, yayinda sauranku su tafi, su kai hatsi don gidajenku da suke yunwa.

  9. Suka sa shi a gidan tsaro sai lokacin da nufin Ubangiji ya nuna musu abin da za su yi da shi.

  10. Sa’an nan Filistiyawa suka fizge shi, suka ƙwaƙule idanunsa suka gangara da shi zuwa Gaza. Da suka daure shi da sarƙoƙin tagulla, sai aka sa shi yana niƙa a kurkuku.

  11. Ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku sa wannan mutum a kurkuku, kuma kada ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa, sai na dawo lafiya.’ ”

  12. Amma sarkin Assuriya ya gane cewa Hosheya mai cin amana ne, gama ya aika da wakilai wurin So sarkin Masar, ya kuma daina aika wa sarkin Assuriya haraji yadda ya saba yi kowace shekara. Saboda haka Shalmaneser ya kama shi ya sa a kurkuku.

  13. Don haka Yehohiyacin ya tuɓe kayan fursuna. Kowace rana kuwa yakan ci abinci a teburin sarki har iyakar ransa.

  14. Sai Asa ya yi fushi sosai da mai duban saboda wannan; ya yi fushi ƙwarai har ya sa aka jefa shi a kurkuku. A lokaci guda kuma Asa ya fara gwada wa mutane azaba.

  15. Ba shakka duk wanda bai yi biyayya da dokokin Allahnka ba, da kuma dokokin sarki ba dole a yanke masa hukuncin kisa, ko hukuncin kora, ko hukuncin raba shi da mallakarsa, ko kuma hukuncin kulle shi a kurkuku.

  16. Bari nishe-nishen ’yan kurkuku su zo gabanka; ta wurin ƙarfin hannunka ka kiyaye waɗanda aka yanke wa hukuncin mutuwa.

  17. don yă ji nishe-nishen ’yan kurkuku yă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.”

  18. Suka raunana ƙafafunsa da sarƙa aka sa wuyansa cikin ƙarafa,

  19. Ka ’yantar da ni daga kurkuku, don in yabi sunanka. Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni saboda alherinka gare ni.

  20. don ka buɗe idanun makafi ka ’yantar da kamammu daga kurkuku kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.

  21. don ku ce wa waɗanda suke cikin kurkuku, ‘Ku fito,’ ga waɗanda suke cikin duhu kuma, ‘Ku ’yantu!’ “Za su yi kiwo kusa da hanyoyi su kuma sami wurin kiwo a kowane tudu.

  22. Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu

  23. ‘Ubangiji ya naɗa ka firist a wurin Yehohiyada don ka lura da gidan Ubangiji; ya kamata ka sa kowane mahaukaci wanda yake yi kamar annabi cikin turu da kuma a kangi.

  24. Sojojin sarkin Babilon a lokacin suna ƙawanya wa Urushalima annabi Irmiya kuwa yana a tsare a sansanin matsara a fadar Yahuda.

  25. Suka yi fushi da Irmiya suka sa aka yi masa dūka aka kuma jefa shi cikin kurkuku a gidan Yonatan magatakarda, gama an mai da gidansa ya zama kurkuku.