Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prisons: Persons under the king's displeasure
Ayoyi game da Persons under the king's displeasure
Ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku sa wannan mutum a kurkuku, kuma kada ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa, sai na dawo lafiya.’ ”
Sai Asa ya yi fushi sosai da mai duban saboda wannan; ya yi fushi ƙwarai har ya sa aka jefa shi a kurkuku. A lokaci guda kuma Asa ya fara gwada wa mutane azaba.
Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka daure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, wadda ya aura.