Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da National Sins

152 ayoyi · 34 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zai kuma ba da Isra’ila saboda zunuban da Yerobowam ya yi, da ya kuma sa Isra’ila suka yi.”

  2. suka kuma bi gurbin al’umman da Ubangiji ya kora a gabansu, da kuma ayyukan da sarakuna Isra’ila suka gabatar.

  3. Isra’ilawa a ɓoye sun aikata abubuwan da ba daidai ba ga Ubangiji Allahnsu. Tun daga hasumiyoyi har zuwa birane masu katanga, sun gina wa kansu wuraren sujada na tudu a dukan garuruwansu.

  4. Suka kafa keɓaɓɓun duwatsu da kuma ginshiƙan Ashera a kowane tudu mai tsayi da kuma a ƙarƙashin kowane babban itace.

  5. Suka ƙona turare a kan kowane tudu, kamar dai yadda al’umman da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka yi muguntan da ya sa Ubangiji ya yi fushi.

  6. Suka bauta wa gumaka, ko da yake Ubangiji ya ce, “Ba za ku yi wannan ba.”

  7. ko Yahuda ma ba su kiyaye umarnan Ubangiji Allahnsu ba. Sun bi gurbin da Isra’ila ta kawo.

  8. Shugabannin Isra’ila da sarki suka ƙasƙantar da kansu suka ce, “Ubangiji mai adalci ne.”

  9. Sa’ad da Ubangiji ya ga sun ƙasƙantar da kansu, sai wannan maganar Ubangiji ta zo wa Shemahiya, “Tun da yake sun ƙasƙantar da kansu, to, ba zan hallaka su ba, amma zan cece su, ba zan kwararo fushina ta hannun Shishak a kan Urushalima ba.

  10. Ya gina masujadan kan tudu a tuddan Yahuda, ya kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, ya sa Yahuda suka kauce.

  11. Yehoram ya sami wasiƙa daga Iliya annabi, wadda ta ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda ya ce, ‘Ba ka yi tafiya a hanyoyin mahaifinka Yehoshafat ko Asa sarkin Yahuda ba.

  12. Amma ka yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, ka sa Yahuda ya kauce, ka kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, kamar yadda gidan Ahab ta yi. Ka kuma kashe ’yan’uwanka, membobi gidan mahaifinka, mutanen da suka fi ka kirki.

  13. “Amma nan da nan, da suka sami hutu, sai suka sāke aikata abin da yake mugu a idonka. Sai ka yashe su ga hannun abokan gābansu don su yi mulki a kansu. Sa’ad da suka yi kuka kuma gare ka, ka ji daga sama, cikin jinƙanka kuma ka fisshe su sau da sau.

  14. Suka zub da jini marar laifi, jinin ’ya’yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana, ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu.

  15. Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu.

  16. Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu;

  17. saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.

  18. Ya sa aka ji tausayinsu a wurin dukan waɗanda suka kame su.

  19. Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi, gama ba a biyayya da dokarka.

  20. Adalci yakan ɗaukaka al’umma, amma zunubi kan kawo kunya ga kowane mutane.

  21. In mai mulki yana sauraran ƙarairayi, dukan ma’aikatansa za su zama mugaye.

  22. Ku kasa kunne, ya sammai! Ki saurara, ya duniya! Gama Ubangiji ya yi magana, “Na yi renon ’ya’ya, na kuma raya su, amma sun tayar mini.

  23. Saniya ta san maigidanta, jaki ya san wurin sa wa dabbobi abinci maigidansa, amma Isra’ila ba su sani, mutanena ba su gane ba.”

  24. Kash, ya ke al’umma mai zunubi, mutane cike da laifi, tarin masu aikata mugunta, ’ya’yan da aka miƙa wa lalaci! Sun yashe Ubangiji; sun rena Mai Tsarkin nan na Isra’ila suka juya masa baya.

  25. Me ya sa za a ƙara yin muku dūka? Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa? An yi wa dukan kanku rauni, zuciyarku duk tana ciwo.