Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Idolatry

447 ayoyi · 205 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, duba waje arewa.” Sai na duba, a mashigin arewa na ƙofar bagaden kuwa na ga wannan gunki na tsokanar kishi.

  2. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwan banƙyamar da gidan Isra’ila ke yi a nan, abubuwan da za su kore ni daga wuri mai tsarkina? Amma za ka ga abubuwan da suka ma fi banƙyama.”

  3. Sa’an nan ya kawo ni mashigin filin. Na duba, na kuma ga rami a bango.

  4. Ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka haƙa cikin bangon.” Da na haƙa cikin bangon sai na ga ƙofar shiga a can.

  5. Sai ya ce mini, “Shiga ka ga mugaye da kuma abubuwa banƙyamar da suke yi a can.”

  6. Na kuwa shiga na duba, sai na ga zāne-zāne ko’ina a bangon na kowane irin abubuwa masu rarrafe da kuma dabbobi masu ƙazanta da dukan gumakan gidan Isra’ila.

  7. A gabansu ga dattawa saba’in na gidan Isra’ila tsaye a cikinsu, Ya’azaniya ɗan Shafan kuwa yana tsaye a cikinsu. Kowa yana da farantin ƙona turare a hannunsa, tulin hayaƙin turare mai ƙanshi ya tunnuƙe zuwa sama.

  8. Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da dattawan gidan Isra’ila suke yi a cikin duhu, kowa yana a ɗakin tsafin gunkinsa? Suna cewa, ‘Ubangiji ba ya ganinmu; Ubangiji ya yashe ƙasar.’ ”

  9. Ya kuma ce, “Za ka gan su suna yin abubuwan da suka fi waɗannan banƙyama.”

  10. Sa’an nan ya kawo ni mashigin arewa na ƙofar gidan Ubangiji, sai na ga mata zaune a can, suna makokin Tammuz.

  11. Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga wannan? Za ka ga abubuwan da suke masu banƙyama fiye da wannan.”

  12. Sa’an nan ya kawo ni cikin fili na cikin gidan Ubangiji, a can kuwa a ƙofar haikali, tsakanin shirayi da bagade, akwai kamar mutum ashirin da biyar. Suka ba haikalin Ubangiji baya suna fuskanta wajen gabas, suna rusuna wa rana a gabas.

  13. Ya ce mini, “Ka ga wannan, ɗan mutum? Ƙaramin abu ne gidan Yahuda su yi abubuwan banƙyamar da suke yi a nan? Dole ne su cika ƙasar da rikici su kuma ci gaba da tsokane ni in yi fushi? Dube su suna tsokanata!

  14. Saboda haka zan hukunta su cikin fushi; Ba zan dube su da tausayi ko kuwa in ƙyale su ba. Ko da yake suna ihu a kunnuwana, ba zan saurare su ba.”

  15. Sai na ji ya yi kira da babbar murya yana cewa, “Kawo matsaran birni a nan, kowanne da makami a hannunsa.”

  16. Na kuma ga mutane shida suna zuwa daga kowane gefen ƙofar ta bisa, wadda take fuskantar arewa, kowanne da makamin kisa a hannunsa. Tare da su akwai mutum saye da lilin yana rataye da jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa. Suka shiga suka tsaya kusa da bagaden tagulla.

  17. To, fa, ɗaukakar Allah na Isra’ila ta haura daga bisa kerubobi, inda ta kasance, ta tashi zuwa bakin madogarar ƙofar haikali. Sai Ubangiji ya kira mutumin da yake saye da lilin wanda ya rataye jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa

  18. ya ce masa, “Ka ratsa birnin Urushalima ka sa shaida a goshin waɗanda suke baƙin ciki da kuma makoki a kan dukan abubuwan banƙyamar da ake yi a cikinsa.”

  19. Yayinda nake saurara, sai ya ce wa waɗansu, “Ku bi shi ta birnin ku kuma kashe, babu tausayi ko kuwa jinƙai.

  20. Ku kashe tsofaffi da samari da ’yan mata, mata da yara, amma kada ku taɓa wani wanda yake da shaida. Ku fara a wuri mai tsarkina.” Saboda haka suka fara da dattawan da suke gaban haikali.

  21. Sa’an nan ya ce musu, “Ku ƙazantar da haikalin ku kuma cika filayen da kisassu. Ku tafi!” Saboda haka suka fita suka kuma fara kisa a duk birnin.

  22. Yayinda suke kisan sai aka bar ni kaɗai, na fāɗi rubda ciki, na yi kuka na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Za ka hallaka dukan raguwar Isra’ila a wannan zafin fushinka a Urushalima?”

  23. Ya amsa mini ya ce, “Zunubin gidan Isra’ila da Yahuda ya yi girma ainun; ƙasar ta cika da rashin adalci. Suna cewa, ‘Ubangiji ya yashe ƙasar; Ubangiji ba ya gani.’

  24. Saboda haka ba zan dube su da tausayi ko kuwa in ƙyale su ba, amma zan kawo wa kansu abin da suka yi.”

  25. Sai mutumin da yana saye da lilin yake kuma rataye da jaka ƙunshe da kayan rubutu a gefensa ya mayar da magana, yana cewa, “Na yi yadda ka umarci ni.”