Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God

662 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba.

  2. Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’

  3. Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya.

  4. Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba.

  5. Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

  6. Ya taimaki bawansa Isra’ila, yana tunawa yă nuna jinƙai

  7. ga Ibrahim da zuriyarsa har abada, kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.”

  8. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.

  9. Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda

  10. (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),

  11. don yă nuna jinƙai ga kakanninmu, yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,

  12. rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,

  13. Sai ya ba su wannan misali ya ce, “Wani mutum yana da itacen ɓaure, da aka shuka a gonar inabinsa. Da ya je cire ’ya’yan itacen, sai ya tarar ba tă yi ’ya’ya ba.

  14. Sai ya ce wa mai lura da gonar inabin, ‘Yau shekara uku ke nan ina zuwa neman ’ya’yan ɓaure daga itacen nan, amma ba na samun kome. Sare shi! Don me za a bar shi ya tare wuri.’

  15. “Mutumin ya amsa ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ka bar shi, in yi masa banƙasa, in kuma zuba masa taki har na shekara ɗaya.

  16. In kuwa ya ba da ’ya’ya shekara mai zuwa, yana da kyau! In kuwa ba haka ba, sai ka sare shi.’ ”

  17. “In ɗayanku yana da tumaki ɗari, sa’an nan ɗayansu ta ɓace. Ashe, ba zai bar tasa’in da tara a fili ya je neman wadda ta ɓace, har sai ya same ta ba?

  18. In ya same ta, zai sa ta a kafaɗa da murna,

  19. ya dawo gida. Sa’an nan zai kira abokansa da maƙwabtansa wuri ɗaya ya ce, ‘Ku taya ni murna, na sami tunkiyana da ta ɓata.’

  20. Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba.

  21. Yesu ya ci gaba da cewa, “Akwai wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza.

  22. Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, ‘Baba, ba ni rabon gādona.’ Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa.

  23. “Bayan ’yan kwanaki, sai ƙaramin ɗan ya tattara kayansa duk, ya tashi ya tafi wata ƙasa mai nisa. A can, ya ɓatar da dukiyarsa duka a rayuwar banza.

  24. Bayan ya ɓatar da kome, sai ga muguwar yunwa a dukan ƙasar, har ya shiga rashi.

  25. Sai ya je ya sami aiki a wurin wani mutumin ƙasar, wanda ya aike shi a gonakinsa, ya yi kiwon aladu.