Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Edomites

154 ayoyi · 14 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Shi ne kuma wanda ya ci mutanen Edom dubu goma a yaƙi, a Kwarin Gishiri, ya kuma ci Sela da yaƙi, ya ba ta suna Yokteyel, sunan da ake kiranta har wa yau.

  2. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta. Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba.

  3. Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki.

  4. Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki.

  5. Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit.

  6. Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki.

  7. Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki.

  8. Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki.

  9. Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab.

  10. Hadad shi ma ya mutu. Manyan Edom su ne, Timna, Alwa, Yetet

  11. Oholibama, Ela, Finon

  12. Kenaz, Teman, Mibzar,

  13. Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom.

  14. A zamanin Yehoram, Edom ya tayar wa Yahuda ya kuma naɗa sarkinsa.

  15. Saboda haka Yehoram ya tafi can tare da shugabannin sojojinsa da kuma dukan keken yaƙinsa. Mutanen Edom suka kewaye shi da shugabannin keken yaƙinsa, amma ya tashi ya fatattaki su da dare.

  16. Har yă zuwa yau Edom na tawaye a kan Yahuda. Libna ya yi tawaye a lokaci guda, domin Yehoram ya yashe Ubangiji Allah na kakanninsa.

  17. Sa’an nan Amaziya ya yi ƙarfin hali ya jagoranci mayaƙansa zuwa Kwarin Gishiri, inda ya kashe mutanen Seyir dubu goma.

  18. Mayaƙan Yahuda suka kuma kama mutane dubu goma da rai, suka ɗauke su zuwa ƙwanƙolin dutsen, suka yi ta tunkuɗa su ƙasa suka yi kaca-kaca.

  19. Abin da Allah ya faɗa game da Duma, Wani ya kira ni daga Seyir, “Mai tsaro, me ya rage a daren? Mai tsaro, me ya rage a daren?”

  20. Mai tsaro ya amsa, “Safiya ta gabato, haka kuma dare. In za ka yi tambaya, to, yi tambaya; sai ka sāke zuwa, ka tambaya.”

  21. Wane ne wannan mai zuwa daga Edom, daga Bozra, saye da jajjayen rigunarsa? Wane ne wannan, sanye cikin daraja, tafe cikin girmar ƙarfinsa? “Ni ne, mai magana cikin adalci, mai ikon ceto.”

  22. Me ya sa rigunanka suka yi ja, sai ka ce na wanda yake tattaka ’ya’yan inabi?

  23. “Na tattake ’ya’yan inabi ni kaɗai; cikin al’ummai kuma babu wani tare da ni. Na tattake su cikin fushina Na matse su cikin hasalata; jininsu ya fantsamar wa rigunana, na kuma ɓata dukan tufafina.

  24. Gama ranar ɗaukan fansa tana a cikin zuciyata, kuma shekarar fansata ta zo.

  25. “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan hukunta dukan waɗanda aka yi musu kaciya kawai a jiki,