Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Edomites: Prophecies concerning

88 ayoyi · 14 fannoni

Ayoyi game da Prophecies concerning

Tace bisa littafi
  1. Ishaku ya amsa wa Isuwa, “Na mai da shi shugaba a kanka, na sa dukan dangoginsa su zama bayinsa, na kuma ba shi hatsi da sabon ruwan inabi. Saboda haka me kuma zan yi maka ɗana?”

  2. Isuwa ya ce wa mahaifinsa, “Iyakar albarkar da kake da ita ke nan, baba? Ka albarkace ni ni ma, baba!” Sai Isuwa ya ɗaga murya ya yi kuka.

  3. Mahaifinsa Ishaku ya amsa masa ya ce, “Ga shi, ni’imar ƙasar za tă nisanci mazauninka. Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za tă nisance ka.

  4. Za ka rayu ta wurin takobi za ka kuwa bauta wa ɗan’uwanka. Amma sa’ad da ka ɓalle, za ka kakkarye karkiyarsa daga wuyanka.”

  5. Abin da Allah ya faɗa game da Duma, Wani ya kira ni daga Seyir, “Mai tsaro, me ya rage a daren? Mai tsaro, me ya rage a daren?”

  6. Mai tsaro ya amsa, “Safiya ta gabato, haka kuma dare. In za ka yi tambaya, to, yi tambaya; sai ka sāke zuwa, ka tambaya.”

  7. Wane ne wannan mai zuwa daga Edom, daga Bozra, saye da jajjayen rigunarsa? Wane ne wannan, sanye cikin daraja, tafe cikin girmar ƙarfinsa? “Ni ne, mai magana cikin adalci, mai ikon ceto.”

  8. Me ya sa rigunanka suka yi ja, sai ka ce na wanda yake tattaka ’ya’yan inabi?

  9. “Na tattake ’ya’yan inabi ni kaɗai; cikin al’ummai kuma babu wani tare da ni. Na tattake su cikin fushina Na matse su cikin hasalata; jininsu ya fantsamar wa rigunana, na kuma ɓata dukan tufafina.

  10. Gama ranar ɗaukan fansa tana a cikin zuciyata, kuma shekarar fansata ta zo.

  11. “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan hukunta dukan waɗanda aka yi musu kaciya kawai a jiki,

  12. Masar, Yahuda, Edom, Ammon, Mowab da dukan waɗanda suke zaune a hamada a wurare masu nisa. Gama dukan waɗannan al’ummai marasa kaciya ne, har dukan gidan Isra’ila ma marasa kaciya ne a zuciya.”

  13. A farkon sarautar Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji.

  14. Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka yi karkiyar itace da maɗaurai ka ɗaura a wuyanka.

  15. Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.

  16. Ka ba su saƙo wa iyayengijinsu su ce, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ku faɗa wa iyayengijinku wannan.

  17. Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama.

  18. Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa.

  19. Dukan al’ummai za su bauta masa da ɗansa da kuma jikansa har sai har lokacin ƙasarsa ya kai; sa’an nan al’ummai masu yawa da kuma manyan sarakuna za su kasance a ƙarƙashinsa.

  20. “ ‘ “Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa.

  21. Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’

  22. Suna muku annabcin ƙaryar ne kawai da za tă kau da ku daga ƙasarku; zan kore ku za ku kuwa hallaka.

  23. Amma duk al’ummar da ta rusuna da wuyarta a ƙarƙashin karkiyar sarkin Babilon ta kuma bauta masa, zan bar al’ummar ta zauna a ƙasarta ta noma ta, ta kuma zauna a can, in ji Ubangiji.” ’ ”

  24. Game da Edom. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Babu sauran hikima a Teman ne? Shawara ta ɓace daga masu basira ne? Hikimarsu ta ruɓe ne?

  25. Ku juya ku gudu, ku ɓuya a cikin kogwanni masu zurfi, ku da kuke zama a Dedan, gama zan kawo masifa a kan Isuwa a lokacin da zan hukunta shi.