Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Edomites: Kings of

17 ayoyi · 14 fannoni

Ayoyi game da Kings of

  1. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki,

  2. Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba.

  3. Sa’ad da Bela ya rasu, Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi.

  4. Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.

  5. Sa’ad da Husham ya rasu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a ƙasar Mowab, ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Awit.

  6. Sa’ad da Hadad ya rasu, Samla daga Masreka ya gāje shi.

  7. Sa’ad da Samla ya rasu, Sha’ul daga Rehobot na ta kogi ya gāje shi.

  8. Sa’ad da Sha’ul ya rasu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi.

  9. Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce ’yar Matired, jikanyar Me-Zahab.

  10. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta. Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba.

  11. Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki.

  12. Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki.

  13. Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit.

  14. Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki.

  15. Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki.

  16. Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki.

  17. Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab.