Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Edomites: Join Babylon in war against the Israelites

9 ayoyi · 14 fannoni

Ayoyi game da Join Babylon in war against the Israelites

  1. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Taya, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom, ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar ’yan’uwa ba,

  2. zan aika da wuta a Taya, da za tă ƙone kagarunta.”

  3. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Edom, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi, babu tausayi, domin ya ci gaba da fusata bai yarda yă huce daga fushinsa ba.

  4. A ranan nan kin tsaya kawai kina zuba ido yayinda baƙi suke washe dukiyar ɗan’uwanki, baƙi kuma suka shiga ta ƙofofinsa suka jefa ƙuri’a don a rarraba Urushalima, kin tsaya kina kallo kamar ɗaya daga cikin abokan gābansa.

  5. Bai kamata ki rena ɗan’uwanki a ranar masifarsa ba, ko ki yi farin ciki a kan mutanen Yahuda a ranar hallakarsu, ko ki yi fariya sosai a ranar wahalarsu.

  6. Bai kamata ki bi ta ƙofofin mutanena a ranar bala’insu ba, ko ki rena su a cikin masifarsu a ranar bala’insu, ko ki ƙwace dukiyarsu a ranar bala’insu ba.

  7. Bai kamata ki tsaya a mararraba don ki kashe waɗanda suke ƙoƙarin tserewa ba, ko ki ba da waɗanda suka tsere ga hannun maƙiyansu a ranar wahalarsu ba.

  8. “Ranar Ubangiji ta yi kusa don dukan al’ummai. Kamar yadda kuka yi, haka za a yi muku; ayyukanku za su koma a kanku.

  9. Kamar yadda kuka sha a kan tuduna mai tsarki, haka dukan al’ummai za su yi ta sha, za su sha, su kuma sha su zama sai ka ce ba su taɓa kasancewa ba.