Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Edomites

154 ayoyi · 14 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Na ƙaunace ku, in ji Ubangiji. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya ka ƙaunace mu?’ “Isuwa ba ɗan’uwan Yaƙub ba ne?” In ji Ubangiji. “Duk da haka na ƙaunaci Yaƙub,

  2. amma na ƙi Isuwa, na kuma mai da ƙasarsa da take kan duwatsu kango, na ba da gādonsa ga dilolin hamada.”

  3. Edom zai iya cewa, “Ko da yake an ragargaza mu, ai, za mu sāke gina kufanmu.” Amma ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Za su iya gini, amma zan rushe. Za a ce da su Muguwar Ƙasa, mutane da kullum suke a ƙarƙashi fushin Ubangiji.

  4. Za ku ga wannan da idanunku ku kuma ce, ‘Ubangiji da girma yake, har gaba da iyakokin Isra’ila ma!’