Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Edomites

154 ayoyi · 14 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka, ku ji abin da Ubangiji ya shirya a kan Edom, abin da ya nufa wa waɗanda suke zama a Teman. Za a ja ƙanana na garken tumaki a tafi; zai hallaka wurin kiwonsu sarai saboda su.

  2. Amon fāɗuwarsu zai sa ƙasa ta girgiza; za a kuma ji muryar kukansu a Jan Teku.

  3. Duba! Gaggafa tana firiya tana kuma saukowa, tana buɗe fikafikanta a bisa Bozra. A wannan rana zukatan jarumawan Edom za su zama kamar macen da take naƙuda.

  4. Ku yi murna da farin ciki, ya Diyar Edom, ke mai zama a ƙasar Uz. Amma ke ma za a ba ki kwaf; za ki bugu ki zama tsirara.

  5. Ya Diyar Sihiyona, hukuncinki zai ƙare; ba zai sa zaman bautarki yă yi tsayi ba. Amma ya Diyar Edom, zai hukunta zunubinki yă tona tsiraicinki.

  6. “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Edom ya ɗauki wa kanta fansa a kan gida Yahuda, ta yi babban laifi ta wurin yin haka,

  7. saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan miƙa hannuna a kan Edom in kashe mutanenta da dabbobinsu. Zan sa ta zama kufai, kuma tun daga Teman har zuwa Dedan za a kashe su da takobi.

  8. Zan ɗau fansa a kan Edom ta hannun mutanena Isra’ila, za su kuwa hukunta Edom bisa ga fushina da hasalata; za su san sakayyata, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”

  9. “Edom tana can, sarakunanta da dukan yerimanta; duk da ikonsu, sun kwanta tare da waɗanda aka kashe da takobi. Suna kwance tare da marasa kaciya, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.

  10. “Dukan yerima arewa da dukan Sidoniyawa suna can; sun gangara tare da waɗanda aka kashe cikin kunya duk da tsoron da suka haddasa ta wurin ikonsu. Sun kwanta tare da marasa kaciya tare da waɗanda aka kashe da takobi suna kuma shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.

  11. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  12. “Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir; ka yi annabci a kansa

  13. ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, Dutsen Seyir, zan kuma miƙa hannuna gāba da kai in mai da kai kango.

  14. Zan mai da garuruwanka kufai za ka kuma zama kango. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.

  15. “ ‘Domin ka riƙe ƙiyayya ta tun dā, ka kuma ba da mutanen Isra’ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, lokacin da adadin horonsu ya cika,

  16. saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sa a zub da jininka zan kuwa fafare ka. Da yake ba ka ƙi zub da jini ba, zub da jini zai fafare ka.

  17. Zan mai da Dutsen Seyir kango in kuma yanke dukan waɗanda suke shiga da fita a cikinka.

  18. Zan cika duwatsunka da matattu; waɗanda aka kashe da takobi za su fāɗi a kan tuddanka, da cikin kwarurukanka, da cikin dukan kwazazzabanka.

  19. Zan mai da kai kango har abada; ba za a zauna a cikin garuruwanka ba. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.

  20. “ ‘Domin kun ce, “Waɗannan al’ummai biyu da ƙasashe za su zama namu za mu kuma mallake su,” ko da yake Ni Ubangiji ina a can,

  21. saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sāka maka gwargwadon fushi da kuma kishin da ka nuna a ƙiyayyarsu da ka yi zan kuma sanar da kaina a cikinsu sa’ad da na hukunta ka.

  22. Sa’an nan za ka san cewa Ni Ubangiji na ji duk abubuwan banzan da ka faɗa a kan duwatsun Isra’ila. Ka ce, “An mai da su kango an kuma ba mu su mu cinye.”

  23. Ka yi fariya a kaina, ka kuma yi magana a kaina ba gaggautawa, na ji shi sarai.

  24. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa yayinda dukan duniya take farin ciki, zan mai da kai kango.

  25. Domin ka yi farin ciki sa’ad da gādon gidan Isra’ila ya zama kufai, haka zan yi da kai, ya Dutsen Seyir, kai da dukan Edom. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ”