Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Church (2)

158 ayoyi · 7 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan za ki duba ki kuma haskaka zuciyarki zai motsa ya kuma cika da farin ciki; za a kawo miki wadata daga tekuna, za a kawo miki arzikin al’ummai.

  2. Manyan ayarin raƙuma za su cika ƙasar, ƙananan raƙuma ke nan daga Midiyan da Efa. Daga Sheba kuma duka za su zo, suna ɗauke da zinariya da turare suna shelar yabon Ubangiji.

  3. Rana ba za tă ƙara zama haskenki a yini ba, balle hasken wata ya haskaka a kanki, gama Ubangiji zai zama madawwamin haskenki, Allahnki kuma zai zama ɗaukakarki.

  4. Ranarki ba za tă ƙara fāɗuwa ba watanki kuma ba zai ƙara shuɗewa ba; Ubangiji zai zama madawwamin haskenki, kwanakin baƙin cikinki za su ƙare.

  5. Sa’an nan dukan mutanenki za su zama masu adalci za su kuma mallaki ƙasar har abada. Su ne reshen da na shuka, aikin hannuwana, don nuna darajata.

  6. Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu

  7. don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu, don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,

  8. in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa.

  9. Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima; ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji, kada ku ba kanku hutu,

  10. kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima ya kuma mai da ita yabon duniya.

  11. Ubangiji ya yi shela ga iyakokin duniya cewa, “Faɗa wa Diyar Sihiyona, ‘Ga Mai Cetonki yana zuwa! Ga ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa yana raka shi.’ ”

  12. Za a ce da shi Tsattsarkar Mutane, Fansassu na Ubangiji; za a kuma ce da ke Wadda Aka Nema Birnin da Ba Za a Ƙara Yashe ta ba.

  13. Kamar yadda uwa takan ta’azantar da ɗanta haka zan ta’azantar da ku; za ku kuma ta’azantu a Urushalima.”

  14. Sa’ad da kuka ga wannan, zuciyarku za tă yi farin ciki za ku kuma haɓaka kamar ciyawa; za a sanar da hannun Ubangiji ga bayinsa, amma za a nuna wa maƙiyansa fushinsa.

  15. “Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona.

  16. Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi.

  17. Za a yi ranar da matsara za su tā da murya a kan tuddan Efraim su ce, ‘Ku zo, bari mu haura Sihiyona, zuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ”

  18. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku rera don farin ciki wa Yaƙub; ku yi sowa don al’ummai da suke nesa. Ka sa a ji yabanku, ku kuma ce, ‘Ya Ubangiji ka ceci mutanenka, raguwar Isra’ila.’

  19. Ku waɗanda kuka tsere wa takobi, ku gudu kada ku tsaya! Ku tuna da Ubangiji a ƙasa mai nesa, ku kuma yi ta tunani a kan Urushalima.”

  20. “Mun sha kunya saboda zargin da ake yi mana kunya ta rufe mu, domin baƙi sun shiga tsarkakan wurare na gidan Ubangiji.”

  21. Hawaye na kwararowa daga idanuna domin an hallaka mutanena.

  22. Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye, ba hutawa.

  23. Har sai in Ubangiji ya duba daga sama ya gani.

  24. Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki domin dukan matan birnina.

  25. A busa ƙaho a Sihiyona, a yi shelar azumi mai tsarki, a kira tsarkakan taro.